Mu koyi turanci (ebook)



Assalamu alaikum, I am Ahmad Aliyu. I would like to use this piece of writing to teach you how to speak English.


A cikin wannan darasin za mu yi ƙoƙarin koyar da yadda ake magana da turanci cikin taƙaitattaun jimloli ga 'yan koyo.

 

I go to work on foot.

Na kan je aiki da ƙafa.


She goes to school by commercial bus.

Ta kan je makaranta a motar haya.


We have our breakfast at 7 o'clock.

Mu kan yi karin kumallo da ƙarfe bakwai.


Have ya na da ma'anoni da dama, ɗaya daga cikin su itace cin abinci, wanda kuma da wannan ma'anar mu ka yi aiki da kalmar have a nan.


I have my lunch at 12 o'clock

Na kan ci abincin rana da ƙarfe sha-biyu.


She has her dinner lately.

Ta kan ci abincin dare amakare.


Go abroad - yin bulaguro zuwa ƙasashen waje

Go shopping - yin siyayya

Go on holiday - tafiya hutu


Abroad

She likes studying abroad.

Ta na son yin karatu a kasar waje.


I studied English Literature abroad.

Na karanci Adabin Turanci a waje.


I won't study abroad since I am poor.

Ba zan yi karatu a waje ba domin ni talaka ne.


Shopping

I like shopping.

Ina son yin siyayya.


I want to go shopping with you.

Ina son zuwa siyayya tare da kai.


She usually shops for clothes.

Ta kan yi siyayyar kayan sanyawa.


He shopped for a new pair of jeans.

Ya siyo sabon wando jins.


Shopping ya na nufin siyayya. Mafi yawan lokaci, a na amfani da kalmar shopping domin nuna yin siyayyar kayan sawa.


Holiday

I really love going to kano on holiday.

Ina matuƙar son zuwa hutu a Kano.


She will go to London on holiday next week.

Sati mai zuwa za ta tafi hutu a London.


Holiday shine hutu da mutum ya kan samu na wani ɗan lokaci a wajen aiki ko kuma ɗalibai a makarantu.


Indoors activities

  • Do the cooking - yin girki
  • Do the ironing - goge kaya
  • Do the laundry - yin wanki
  • Do the dishes - yin wanke-wanke.
  • Do the housework - yin aikace-aikacen gida.


My sister does the cooking once a day.

'Yar uwata ta kan yi girki sau ɗaya a rana.


I do the cooking myself.

Na kan yi girki da kaina.


He does the ironing on the weekends.

Ya kan goge kayansa a ƙarshen sati.


Fatima does the laundry twice a week.

Fatima ta kan yi wanki sau biyu a sati.


We will not do the laundry this week.

Satin nan ba za mu yi wanki ba.


I will pay you to do the dishes.

Zan biyaku ku yi wanke-wanke.


Kalmar You ta na nufin kai (namiji) ko kuma ke (mace) ko kuma ku (maza da yawa) ko kuma ku (mata da yawa).


Amina does not want to do the dishes.

Amina ba ta son yin wanke-wanke.


Have a shower - yin wanka

I have a shower before going to bed.

Na kan yi wanka kafin na kwanta.


She has a shower every morning.

Ta kan yi wanka kowace safiya.


  • Make the bed - gyara gurin kwanciya (gado)
  • Make breakfast - shirya abincin safe
  • Make lunch - shirya abincin rana
  • Make dinner - shirya abincin dare


Breakfast shine abincin da ake ci da safe, lunch shine abincin da ake ci da rana, dinner kuma abincin dare. A mafi yawan lokaci, a kan yi amfani da kalmar have tare da waɗannan a maimakon kalmar eat.


I ate my dinner lately last night.

I had my dinner lately last night.

Jiya da dare na ci abincin dare a makare.


Kalmar eat anfi amfani da ita tare da sunan abinci.


I eat spaghetti.

Na kan yi taliya.


She eats macaroni.

Ta kan ci makaroni.


  • Catch the bus - shiga bas
  • Get on the bus - shiga bas 
  • Catch the train - shiga jirgin-ƙasa
  • Get on the train - shiga jirgin-ƙasa 
  • Get off the bus - sauƙa daga bas
  • Catch someone's attention 
  • get a job - samun aikin yi
  • get fired - kora daga wajen aiki
  • get a chance - samun damar yin wani abu
  • get dressed - sanya kayan sawa

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post