Article wasu kalmomi ne da ake amfani da su tare da wani suna. Wadannan kalmomi su kan yi wani karin haske ga wannan suna sananne ne ko kuma ba sananne ba ne. Amma kafin mu yi nisa a cikin darasin ya na da kyau, ka yi subscribe na wannan tasha ta koyan turanci. Domin yin hakan shi zai baka damar samun sakwan imel a duk lokacin da mu daura sabon darasi a wannan tasha.
Yanzu kuma sai mu ci gaba da darasin mu. Article su ne a, an da kuma the. Wadannan kalmomi kan zo tare da suna wato noun.
Misali
a pen - biro
a book - littafi
an apple - tufa
an orange - lemu
the aeroplane - jirgin sama
the helicopter - jirgi mai saukar angulu
Dalibai da dama kan yi kuskure wajen furta a, sai ka ji su na cewa e. Misali, maimako a book sai ka ji sun ce e book. Wanda hakan kuskure wajen furta kalma turanci.
Idan kalma ta fara da harafin da ke da sautin baki, sai a yi amfani da harafin a tare da ita, kaman wadannan kalmomin cup, ruler, phone da pencil.
Misali
a cup - kofi
a ruler - rula
a phone - wayar salula
a pencil - fensir
Idan kuma kalma ta fara da harafin da ke da sautin wasali, sai a yi amfani da kalmar an tare da ita, kaman wadannan kalmomin actor, actress da kuma author.
Misali
an actor - dan wasan kwaikwayo
an actress - 'yar wasan kwaikwayo
an author - mawallafi
an authoress - mawallafiya
Sannan kuma akwai wasu kalmomi da za ka samu sun fara da harafin wasali, amma kuma wajen furuci za ka ji a na furta su da sautin baki. Misalin irin waɗannan shine U-turn, urine, unicorn, uniform, user, utensil, unit da kuma university.