Yadda ake tambaya da Turanci

Assalamu alaikum. Mai karatu barka da wannan lokaci. Muna fatan kana farin ciki tare da jin daɗin kasancewa da wannan shafi. Haka kuma, muna fatan waɗannan darusa da muke wallafawa zasu kasance masu amfanarka da duk wanda ya karantasu. Allah yasa haka, Amin. A wannan darasi zamu yi bayani ne akan yadda ake tambaya da Turanci.



Domin yin tambaya da Turanci, kana buƙatar sanin kalmomin da ake amfani dasu wajen yin tambayar da kuma yadda ake yin tambayar dasu. Kamar dai sauran harsunan duniya, tambaya na ɗaya daga cikin maganganun da mutane suke yawaita yi. Domin neman ilimi ko ƙarin haske game da wani mutum, ko game da wani abu da ya shige musu duhu.


Waɗannan kalmomi dake jere a ƙasa, kalmomi ne da ake amfani dasu domin yin tambaya da Turanci. Saboda haka, samun ƙarin haske game da yadda ake aiki dasu abu ne mai matuƙar muhimmanci ga ɗalibai da sauran waɗanda suke son koyan Turanci. Kalmomin sune:


    1. How (ya ya, ya ake ciki)
    2. How many (tambayar adadi)
    3. How much (tambayar farashi)
    4. What (mene, mene ne, meye)
    5. When (yaushe, wane lokaci)
    6. Where (ina)
    7. Which (waɗanne, wanne, wacce)
    8. Who (waye, wane ne, wace ce)
    9. Why (tambayar dalili)


Ga kuma bayanin yadda ake amfani da kalmomin daki-daki:


Kalmar HOW

Wannan kalma ta kanzo a farkon jimla, sannan sauran ɓangarorin jimlar suzo. Kalmar how ana amfani da ita domin tambaya kamar cewa: ya ya, ƙa ƙa, ya ake yin kaza-kaza. Misali:


    1. How to draw with a pencil? (Ta ya ya ake yin zane da fensir?)
    2. How old are you? (Shekarunka nawa?)

Hakama, ana amfani da kalmar wajen tambayar halin da mutum yake ciki a lokacin da ake gaisawa:


    1. How are you? (Ya kake?)
    2. How is the work? (Ya aiki?)
    3. How is it going? (Ya ake ciki?)


Har-ila yau, ana amfani da kalmar how domin tambayar yadda wani yayi wani aiki. Misali:


    1. How do you get to school? (Ta yaya kake tafiya makaranta)
    2. That's amazing drawing! How did you draw it? (Kai wannan zanen yayi matuƙar kyau. Ta yaya ka zanashi?)

Kalmar HOW MUCH

Kuma dai, ana amfani da kalmar how tare da kalmar much domin tambayar farashin wani abu. Misali:


  • What a wonderful bicycle! How much did you buy it? (Kai gaskiya wannan keken ya haɗu sosai! Nawa ka siyoshi?)

Kalmar HOW MANY

Daga karshe, ana amfani da kalmar how tare da kalmar many domin tambayar adadi. Sai dai abun dubawa anan shine, sunan da zai zo a bayan kalmar many dole ne ya kasance jam'i. Wato idan za a tambayi nawa ne yawa ko adadin wani abu ko wasu mutane. Misali:


    1. How many people can lift a car? (Mutane nawa ne zasu iya ɗaga mota?)
    2. How many animals did you see at the zoo? (Dabbobi nawa ka gani a gidan namun dajin?)
    3. I don't know how many bottles we drank at the party (Ban san ko kwalabe nawa muka sha a wajen bikin ba)

Kalmar WHAT

Kalmar what ana amfani da ita wajen yin tambaya a gurare mabambanta. Wani lokaci zaka samu tana nufin: mene ko mene ne ko meye. Wani lokacin kuma zaka samu tana nufin: ya ake ciki ko ya ya akayi ne ko kuma meke faruwa. Kamar dai yadda zamu gani a misalai da suke tafe:


    1. What is it going? (Meke faruwa?)
    2. What is your name? (Ya ya sunanka?)
    3. What is your favourite film? (Wane fim kafiso?)

What TIME

Sannan ana amfani da kalmar what tare da kalmar time domin tambayar lokaci. Misali:


    1. Oh! It is about to be late. What time is it? (Kaash! Mun kusa makara fa. Ƙarfe nawa ne yanzu?)
    2. What day is it today? (Yau yaushe ne?)
    3. What day was it yesterday? (Jiya yaushe ne?)


Kalmar WHEN

Kalmar when ana amfani da ita wajen tambayar lokaci. Sai dai ba lokaci na agogo ba. Wato idan za a tambayi ƙarfe nawa, sai dai ayi amfani da kalmar what, kamar yadda bayani ya gabata a sama. Amma idan za a tambayi yaushe ne ko wace rana ce za ayi wani biki ko taro, sai dai ayi amfani da kalmar when.


    1. When is your birthday? (Wace rana ce ranar murnar zagayowar haihuwarka?)
    2. When are we traveling abroad? (Yaushe ne zamu yi bulaguro ƙasashen waje?)
    3. When she told you that? (Yaushe ta faɗama naka?)


Kalmar WHERE

Kalmar where ana amfani da ita domin tambayar gurare. Wato idan zaka tambayi ina ne guri kaza ko kuma a wane guri ake yin kaza, sai kayi amfani da kalmar where. Misali:


    1. Where does the school locate? (A ina makarantar take?)
    2. Where bread are made? (A ina ne a yin burodi?)
    3. Where are you going? (Ina zaka je?)


Kalmar WHICH

Kalmar which ana amfani da ita domin yin tambayar rabbabewa a tsakanin ababe mabambanta. Misali, idan za ace wanne kake nufi ko wanne kafi so ko wacce kake nufi. Misali:


    1. That car is mine. (Waccan motar tawa ce)
    2. Which of these cars do you mean is yours? (Wacce cikin motocin nan kake nufi taka ce?)
    3. Which is the best hotel among the three? (Wane otal ne yafi kowanne a cikin su ukun?)


Kalmar WHO

Kalmar who tana nufin waye ko wane ne ko wace ce ko su wane ne ko su wace ce.


    1. Who is your best friend? (Wane ne babban abokinka?)
    2. Who can lift this load? (Waye zai iya ɗaga wannan kayan?)
    3. Who made this delicious meal? (Wace ce ta girka wannan abincin mai ɗan karen daɗin?)


Kalmar WHY

Kalmar why ana amfani da ita wajen tambayar dalili. Ma'ana tana nufin: me yasa ko a dalilin me, a kayi kaza-kaza. Wato idan za a tambayi dalilin da yasa akayi wani aiki da Turanci, akan yi amfani da kalmar why. Kamar sauran kalmomin da bayanansu suka gabata a sama, ana amfani da kalmar why ne a farkon jimla. Misali:


  1. Why you did not go to work yesterday? (Me yasa jiya bakaje aiki ba?)
  2. Why are you crying? (Me yasa kake kuka?)
  3. Why you don't eat meat? (Me yasa baka cin nama?)


Bayan waɗannan kalmomin akwai kalmomin do da have da wasunsu waɗanda suma akan yi amfani dasu domin yin tambaya da Turanci.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post