Yadda ake gina JIMLA SASSAUƘA da turanci

Jama'ar wannan shafi, Assalamu alaikum. Barkanmu da sake kasancewa daku wani sabon darasi wanda acikinsa zamu yi muku bayani akan yadda ake gina jimla sassauƙa da turanci. Shin ko kun san ta yadda zaku fara koyan Turanci?



A cikin darasin nan zamu yi muku bayanin, mene ne jimla sassauƙa, tare da ɓangarorinta da kuma kawo misalai a sauƙaƙe.


Mece ce Jimla Sassauƙa?

Jimla sassauƙa wata jimla ce dake magana ko bayani game da wani abu ko wani aiki guda ɗaya da aka yi.


Jimla sassauƙa ta ƙunshi ɓangarori guda uku, waɗanda sune mai aiki wato aikau (subject). Sai aikin da kansa wato aikatau (verb). Sai kuma wanda aikin ya faɗa a kansa wato karɓau (object). Ga wasu misalai da zamu yi sharhi a kansu domin mai karatu ya fahimci inda aka dosa a darasin.


Misalan sune:

  • Na tuƙa sabuwar motar . (Aliyu ya bugi ƙwallon)


Shin ko kun san yadda ake amfani da kalmar WOULD?


A jimla ta farko wato wadda take cewa "na tuƙa mota". Wannan jimla ta ƙunshi ɓangarori guda uku. Na farko shine mai aiki, na biyu shine aikin da aka yi, na uku kuma shine wanda aikin ya faɗa a kansa.


Bari mu faɗaɗa bayanin sosai domin mai karatu ya fahimci waɗannan muhimman bangarori da ake samunsu a kowace cikakkiyar jimla mai ma'ana.


Ɓangare na farko shine wanda ya yi aikin. Wanda shi ake kira aikau, wato subject da Turanci.


Sai ɓangare na biyu wanda shine aikin da aka yi, wato aikatau. Wanda shi ake kira verb da turanci.


Sai ɓangare na uku wato wanda aikin ya faɗa kansa. Wanda shi ake kira karɓau, wato object da turanci.


Jimla sassauƙa a Turanci n Inglishi ta ƙunshi subject, verb da kuma object - wato aikau, aikatau da kuma karɓau.


Bari mu ɗakko waɗancan misalai da mu ka bayar a farko, sai mu yi sharhinsu daki-daki tare da ɓangarorinsu.


Jimla ta farko ta ce "Na tuƙa mota" a wannan jimla nine subject (wato aikau) ma'ana nina yi aikin da ake magana akansa a cikin jimlar.


Sai tuƙin mota wanda shine verb (wato aikatau). Ma'ana shine aikin da na yi, wanda kuma shine jimlar take magana akai.


Sai kuma motar da na tuƙa. Wacce ita ce object (wato karɓau). Ma'ana ita ce ta karɓi sakamakon aikin da na yi ko kuma ita ce aikin da na yi ya faɗa kanta.


Hakama a jimla ta biyu, wato "Aliyu ya bugi ƙwallon".


A wannan jimlar kuma Aliyu shine subject (wato aikau, ma'ana shine wanda ya yi aikin).


Bugun ƙwallon da ya yi shine verb (wato aikatau, ma'ana shine aikin da ya yi).


Sai kuma ƙwallon, wadda ita ce object (wato karɓau, ma'ana ita ce aikin ya faɗa akanta).


Idan za a gina jimla, sai an fara kawo subject, sai a kawo verb, sannan a kawo object - kamar dai yadda bayani ya gabata. Wannan shine bayanin yadda ake gina jimla sassauƙa da turanci.


Ga sauran misalan na tafe tare da sharhunansu a taƙaice:


  • Musa made a new chair. (Musa ya haɗa sabuwar kujera)


A nan Musa ne subject, made shine verb, sai kuma chair ita ce object.


  • She peels yam every week. (Ta kan fere doya kowane sati)


A nan SHE, wato ita shine subject, peel shine verb, sai kuma yam ita ce object.


  • We broke our vase mistakenly. (Mu fasa robar ajiye filawarmu bisa kuskure)


A nan kuma WE, wato mu shine subject, broke shine verb, sai kuma vase ita ce object.


Vase wata roba ce ko tukunya da ake zuba ƙasa, laka ko yashi acikinta, sannan a dasa wata shuka, ko wata itaciya ko wata fulawa.


  • They beat the thief. (Sun daki ɓarawon)


A nan kuma THEY, wato su shine subject, beat shine verb, sai kuma thief shine object.


Tambaya:

  • The hunter caught a rabbit. (Mafaraucin ya kama zomo)


A nan kuma waye subject, ina verb ɗin yake, sannan mene ne ko wane ne object ɗin? Indai anfahimci darasin, sai a amsa mana wannan tambaya da muka yi a misalin nan na ƙarshe.


Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da kalmar ENVIOUS?

Zamu dakata a nan, muna fatan ana jin daɗin kasancewa da wannan shafi. Muna da wasu darussan ga masu sha'awar koyan Turanci a sauƙaƙe. Ka da a manta ayi like, tare da rarraba darasin ta WhatsApp, Facebook, Telegram, Twitter da sauransu, domin wasu su gani su amfana.


Sannan ka da kuma a manta, idan ba ayi subscribe na channel ɗinmu ba, ayi ƙoƙari, ayi subscribe domin samun sabbin bidiyoyinmu a duk lokacin da mu ka ɗaura, sai mun sake ganinku. Mun gode.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post