Assalamu alaikum, masu bibiyar wannan shafin. Barkan mu da warhaka da kuma sake kasancewa a wani sabon darasi wanda a cikinsa za mu kawo jerin wasu kalmomi da ake amfani da su domin bayyana siffar wani abu ko kuma wani mutum a turanci.
Waɗannan kalmomin da za mu jero a ƙasa a na amfani da su wajen siffanta wani mutum ko wani a lokacin da ake magana da turanci. Saboda haka, waɗannan kalmomin su na da matuƙar mahimmanci ga masu sha'awar koyan turanci.
Misali:
A strong wall
katanga mai ƙarfi
A famous person
sanannan mutum
A beautiful house
gida mai kyau
An old building
tsohon gini
An expensive car
mota mai tsada
A new pair of shoes
sabon takalmi
A new pair of scissors
sabon almakashi
A new pair of jeans
sabon wandon jins
Aliyu is a brave boy.
Aliyu yaro ne jarumi.
The food was so spicy.
Abincin ya da yaji sosai.
The hotel is tall.
Hotal ɗin dogo ne.
Ahmad is a kind guy.
Ahmad saurayi ne mai kirki.
Ga sauran kalmomin
- beautiful - mai kyau, kyakkyawa
- handsome - mutumin kirki
- kind - mai kirki
- tall - dogo, mai tsayi
- short - gajere, guntu
- old - tsoho
- new - sabo
- young - matashi
- strong - mai ƙarfi, ƙaƙƙarfa
- weak - mai rauni
- brave - jarumi
- coward - rago
- simple - mai sauƙin yi
- hard - mai wahala
- expensive - mai tsada
- cheap - mai arha
- difficult - mai wahala
- rich - mai kuɗi, attajiri
- poor - talaka
- fat - mai jiki, mai ƙiba
- thin - siriri
- stupid - banza, wawa
- mad - mahaukaci
- arrogant - mai girman kai
- humble - mai sauƙin kai
- patient - mai haƙuri
- honest - mai gaskiya
- mean - mugu
- crazy - mutumin banza
- generous - mai kyauta, mutumin kirki
- miser - marowaci
- ready - wanda ya shirya
- reluctant - wanda bai shirya ba
- lazy - malalaci
- dirty - mai datti, mai dauɗa
- clean - wankakke, tsaftatacce
- straight - miƙaƙƙe
- bend - lanƙwasasshe, wanda ya lanƙwashe
- spicy - mai yaji
- sugary - mai zaƙi
- sour - mai tsami
- bitter - mai ɗaci
- salty - mai gishiri
- hot - mai zafi
- cold - mai sanyi
- oily - mai maiƙo
- soft - mai laushi
- rigid - mai tauri
- beloved - wanda ake so sosai
- famous - sananne
- fast - mai gudu sosai
- quick - mai sauri
- slow - mara sauri
- far - mai nisa
- near - na kusa
- happy - mai farin ciki
- sad - wanda ba ya cikin farin ciki
- wet - jiƙaƙƙe
- dry - busasshe
- heavy - mai nauyi
- light - maras nauyi
- wide - mai faɗi
- narrow - mai matsi