Yadda a ke amfani da kalmar WOULD

Kalmar would ɗaya ce daga cikin kalmomin verb da ake kira Modal verbs ko kuma Modals a taƙaice. Would verb ne da ake aiki da shi a gurare mabambanta. Ma'anar da kalmar ta ke ɗauka, ta dogara ga muhallin da aka yi amfani da ita. Domin akwai hanyoyi da dama da ake aiki da wannan kalma a Turanci.
Kalmar would kamar sauran Modals, ba ta canzawa a Present tense ko Past tense. Mutane da dama su kan yi tunanin cewa kalmar would, Past particle ɗin kalmar will ce kaɗai. Sai dai ba haka ba ne, ɗaya daga cikin amfanonin kalmar would shine yin aiki a matsayin Past particle ɗin will, wato will a shuɗaɗɗen lokaci. Domin would verb ne mai zaman kansa, hakama will.


Yadda ake sarrafa kalmar would

Sarrafa would ya na da matuƙar sauƙi fiye da sauran verb. Domin ita kalmar would ba ta canzawa, kamar yadda sauran verb ke canzawa duba da canzawar lokaci ko kuma duba da mai aiki. Sauran verb ɗin su kan canza dalilin mai aiki ko shuɗewar lokaci. Misali, kamar: I go, you go, he goes. Kalmar would ba haka ta ke ba. Saboda kalmar ta kan zo a yadda ta ke a ko da yaushe a ko ina. Bari mu ga waɗannan misalai dake tafe:

Affirmative

    1. I would
    2. You would
    3. He would
    4. She would
    5. It would
    6. They would
    7. We would


Idan za a canza mafi yawan verb daga positive zuwa negative, kawai kalmar do not ake rubutawa a tsakanin subject da verb ɗin sentence ɗin. Misali, kamar daga: I play the violin. Zuwa: I do not play the violin. To idan za a canza modals zuwa negative, kalmar not ɗin kaɗai ake ƙarawa a gaban modal verb ɗin. Misali, kamar daga: He would go zuwa He would not go. Ga sauran misalan a tafe:

Negative

    1. I would not
    2. You would not
    3. He would not
    4. She would not
    5. It would not
    6. They would not
    7. We would not


Idan kuma za a canza wata jimla zuwa tambaya, akan sa kalmar do ko does ne a farkon jimlar, sai kuma a canzawa subject da verb guri. Wato verb ɗin ya koma wajen subject, hakama subject ɗin ya koma wajen verb. Sannan sai a sa alamar tambaya a ƙarshen jimlar. Misali, kamar daga: I play the violin. Zuwa: Do I play the violin?


Ba wai kalmomin do ko does ne kaɗai ake aiki da su domin yin tambaya ba. Akwai kalmomin WH da sauran su. Kalmomin WH su ne what (me ye), when (yaushe), where (ina), which (wanne), who (waye), why (me ya sa) da kuma how (ya ya). Waɗannan kalmomin duk a kan yi amfani da su kaman yadda ake aiki da do da does.


Su modals ba a saka kalmar do ko does a farkon jimla, idan za a canza su zuwa tambaya. Modal verb ɗin ake canzawa guri da subject ɗin. Misali, kamar daga: He would go. Zuwa: Would he go?

Interrogative

    1. Would I ... ?
    2. Would you ... ?
    3. Would he ... ?
    4. Would she ... ?
    5. Would it ... ?
    6. Would they ... ?
    7. Would we ... ?


Sannan su ma modal verbs a kan yi amfani da kalmomin WH tare da su domin yin tambaya. Kalmomin WH su ne what, when, where, which, who, why da kuma how. Waɗannan kalmomin duk a kan yi amfani da su a farkon jimla ne idan za a yi tambaya da su. Ga nan misalan yadda ake amfani da kalmomin WH tare da would idan za a yi tambaya.


Kalmomin WH

    1. What would I ... ?
    2. What would you ... ?
    3. What would he ... ?
    4. What would she ... ?
    5. What would it ... ?
    6. What would they ... ?
    7. What would we ... ?


Sannan kuma kalmar aikin da ke biyo bayan would dole ta kasance bare infinitive. Infinitive shi ne verb a asalin yadda yake kafin a sarrafa shi da wani lokaci ko mai aiki. Infinitive shi ne verb tare da kalmar to. Bare infinitive kalma ce ta aiki a asalin ta, amma ba tare da kalmar to ɗin ba. Misali, kamar: to eat zai koma eat, to sit zai koma sit.


A lura:

  • Ba a cewa: I would to eat my lunch. Sai dai a ce: I would eat my lunch.
  • Ba a cewa: I would to play football. Sai dai a ce: I would play football.
  • Ba a cewa: I would to play the violin. Sai dai a ce: I would play the violin.
  • Ba a cewa: I would to run for 5km. Sai dai a ce: I would run for 5km.

  • Waɗannan hanyoyi su ake bi wajen sarrafa wannan kalma. Yanzu kuma bari mu duba hanyoyi da ake aiki da shi.


    Hanyoyin da a ke amfani da WOULD

      1. Reporting will
      2. Past habit
      3. Hypothetical situation
      4. To need to
      5. Requesting


    Reporting will as past

    Ɗaya daga cikin ma'anonin kalmar would, ita ce aiki a matsayin past tense ɗin will. Wato idan ka na bayar da labarin wani abu da ya faru a baya, duk inda kalmar will take, sai ka goge ta ka rubuta kalmar would a wajen. Misali, kamar daga: I will go to market, zuwa: I would go to market.


    • Idan wani ya ce: I will travel to Sokoto. Kai kuma a lokacin da ka ke bayar da labarin sai ka ce: He would travel to Sokoto.


    Misali:

      1. Present: I will visit you. (Zan ziyarceka.)
      2. Past: I would visit you. (Zan ziyarceka.)
      3. Present: I will not give you the money. (Ban zan baka kudin ba.)
      4. Past: I would not give you the money. (Ba zan baka kuɗin ba.)
      5. Present: I will sell my phone. (Zan siyar da wayata.)
      6. Past: I would sell my phone. (Zan siyar da wayata.)
      7. Present: He will play the ukulele later. (Zai kaɗa ukulele nan gaba.)
      8. Past: He would play the ukulele later. (Zai kaɗa ukulele nan gaba.)
      9. Present: They will visit us. (Za su ziyartar mu.
  • Past: They would visit us. (Za su ziyartar mu).

  • Past habit

    A na amfani da would domin nuna wani aiki ko wasu ayyuka da mutum ya kan yawaita yi a wani lokaci da ya wuce a baya. Ma'ana wani aiki wanda a da can baya ka kan yi. Kaman ka ce: lokacin da nake ɗan makaranta na kan je makaranta a makare. Ka ga wannan wani aiki ne da ka ke yawan yi a can baya kafin yanzu.


    Misali:

      1. When I was teenager, I would play football. (Lokacin ina ƙarami na kan yi wasan ƙwallon ƙafa.)
      2. When we were students, we would go to school lately. (Lokacin muna ɗalibai mu kan je makaranta a makare.)
      3. When she kid, she would cry for 30 minutes. (Lokacin tana ƙarama takanyi kukan minti 30.)
      4. When they are in Kano, they would not go to school. (Lokacin da suke Kano ba sa zuwa makaranta.)
      5. When you were 18, you would swim all day. (Lokacin ka na ɗan shekara 18 ka kan wuni ka na iyo.)

    Hypothetical situation

    Hypothetical situation shi ne abun da bai faru ba a zahiri. Sai dai a ce da a ce kaza ya faru ai da na yi kaza. Hypothetical situation da Hausa shi ne da a ce kaza da kaza-kaza.


    Misali:

      1. If I lived in Katsina, I would visit Kusugu Well of Daura. (Idan da na zauna a Katsina, da sai na ziyarci Rijiyar Kusugu da ke Daura.)
      2. If we were the rich, we would travel to Paris. (Idan da mu masu kuɗi ne, da sai mun je birnin Faris.)
      3. If they come early, they would have breakfast with us. (Idan da sun zo da wuri, da mun ci abin safe tare da su.)
      4. If he works hardly, he would succeed. (Idan da ya yi aiki tuƙuru, da sai ya yi nasara.)


    Need to

    A kan yi amfani da kalmar would domin nuna buƙatar wani abu ko yin wani abu. Misali, kamar ka ce: Ina son cin abincin Turawa ko Ta na son zuwa Kano. A Turanci a kan yi amfani da kalmar want to domin faɗin haka. Sannan kuma kalmar would ma a ana amfani da ita wajen bayyana hakan. Maimakon mutum ya ce: I want to buy, sai kawai mutum ya ce: I would like to buy.


    Idan za a yi amfani da kalmar would domin nuna buƙatar wani abu ko bukatar yin wani abu akan haɗa would da kalmar like. Wato would like sai abun da za a yi ya zo bayan su.


    Misali:

      1. I would like to study in the United Kingdom. (Ina son yin karatu a Burtaniya.)
      2. He would like to eat fried yam. (Ya na son ya cin soyayyar doya.)
      3. She would like to buy new dress. (Ta na son siyan sabon kaya.)
      4. They would like give her a gift on her birthday. (Su na son bata kyauta a bikin ranar haihuwar ta.)
      5. We would like to have our dinner in the restaurant. (Mu na son cin abincin dare a shagon abincin.)


    A misalan da su ke sama za a iya cire kalmomin would like a dukkan jimlolin a maye gurbin su da kalmar want kuma duk za su bayar da ma'ana ɗaya.


    Requesting

    A kan yi amfani da kalmar would domin yin tambaya ko rokon wani cikin ladabi.


      1. Would you mind borrowing me your phone? (Dan Allah ba ni aron wayarka)
      2. Would you mind washing my clothes? (Dan Allah ka wanke mun kayan sawa na)
      3. Would you mind teaching them how to speak English? (Dan Allah ka koyar da su yadda ake magana da Turanci)
      4. Would you mind having dinner with me? (Dan Allah za mu ci abincin dare a tare)
      5. Would you mind buying her a new phone? (Dan Allah ka siya mata sabuwar waya)
      6. Za mu tsaya a nan, da fatan darussan da mu ke wallafawa su na amfanar ku.
    Post a Comment (0)
    Previous Post Next Post