Yadda ake amfani da launuka a Turanci

Assalamu alaikum, jama'a. Barkan mu da sake kasancewa a wani sabon darasi na koyan Turanci, wanda a cikin sa za mu yi bayanin wasu launuka tare da nuna yadda ake amfani da su domin bayyana launin wani abu da Turanci. Misali, kamar ka ce: Jar riga, baƙar mota, farar hula da sauran su.
A cikin darasin nan za mu yi bayani daki-daki domin mai karatu ya koyi yadda zai bayar da labarin wani abu da ya gani ta hanyar futo da launinsa ga waɗanda ya ke bawa labarin. Kafin mu yi nisa a cikin darasin, ya na da kyau, ku je shafin YouTube, ku binciko Arewapot, sai ku yi subscribe, tare da taɓa alamar ƙararrawa. Yin hakan shi zai baku damar samun saƙwannin imel a duk sa'adda mu ka yi sabon darasin koyan Turanci.


Da farko, ga sunayen wasu launuka:

    1. White - fari, fara, farare
    2. Black - baƙi, baƙa, baƙaƙe
    3. Ash - ruwan toka
    4. Red - ja, jajaye
    5. Green - kore, koriya, koraye, tsanwa
    6. Blue - shuɗi, shuɗiya, shuɗaye, bla
    7. Yellow - ɗorowa, yalo
    8. Orange - ruwan lemu
    9. Pink - ruwan hoda
    10. Golden - ruwan gwal
    11. Silver - ruwan silba


Ga misalai a kan yadda a ke amfani da launuka da Turanci. Ya na da kyau a sani cewa a Turanci idan za a faɗi kalar wani abu sai an fara kawo sunan kalar, sannan sai a kawo sunan abun da ake kwatantawa.


Misali:

    1. a white book - farin littafi
    2. a white bag - farar jaka
    3. a black dog - baƙin kare
    4. a black cat - baƙar mage
    5. a red chair - jar kujera
    6. a red table - jan tebur
    7. a green pencil - koren fensir
    8. a green ruler - koriyar rula
    9. a blue car - shuɗiyar mota
    10. a blue bicycle - shuɗin keke
    11. a yellow bench - benci ruwan ɗorowa
    12. a yellow chair - kujera ruwan dorowa


Sai kuma na biyu, ya na da kyau a sani cewa a Turanci launuka ba su da jinsi kamar yadda suke da su a Larabci, Faransanci da Hausa. Misali, a Hausa mota ta na jinsin mata, keke kuma jinsin maza. A Turanci ba haka abun yake ba. Idan ka ce white, ya na nufin fari ko fara ko farare; black ya na nufin baƙi ko baƙa ko baƙaƙe; red kuma ja ko jajaye da sauran su.


Misali:

    1. a blue car - shuɗiyar mota
    2. a blue bicycle - shuɗin keke
    3. a black dog - baƙin kare
    4. a black cat - baƙar mage


Idan mu ka dubi waɗannan misalai, za mu ga cewa a misalai biyu na farkon kalmar blue ba ta canza ba, duk da cewa a misali na farko ta zo kafin sunan da ke jinsin mata, hakama a misali na biyu kalmar blue ɗin ba ta canza ba, duk da cewa ta zo ne kafin sunan da ke jinsin maza. A Turanci launuka ba su da jinsi, za ka iya amfani launi ɗaya a sunan da ke jinsin maza ko mata, kamar yadda misalai su ka gabata a sama.


Na uku kuma ya na da kyau a sani cewa a Turanci launuka ba su da jam'i kamar yadda suke da jam'i a Larabci, Faransanci da Hausa. Misali, a Hausa jam'in fari shine farare; jajaye shi ne jam'in ja; baƙaƙe shi ne jam'in baki. Idan ka ce: red da turanci ya na nufin ja guda ɗaya, ko jajaye; green ya na nufin kore, ko koriya ko koraye; blue na nufin shuɗi, ko shuɗiya ko shuɗaye.


Sannan kuma a Turanci sunan abun da kake bayar da labarin sa shi ne ya ke canzawa daga tilo zuwa jam'i. Idan ka ce a red book ya na nufin jan littafi; red books kuma jajayen littattafai. Idan mu ka lura za mu ga cewa kalmar red ba ta canza ba a waɗannan misalai, duk da cewa a misalin farko kalmar ta zo kafin sunan littafi ɗaya, a misali na biyu kuma ta zo kafin sunayen littattafai da yawa. Ga sauran misalan na tafe.


Misali:

    1. red windows - jajayen tagogi
    2. red doors - jajayen ƙofofi
    3. green pencils - korayen fensira
    4. green rulers - korayen ruloli


Idan mu ka sa ido sosai a waɗannan misalai za mu ga cewa a Turanci sunan launukan bai canza ba. Sunayen da a ke nuna launukan su su ne kaɗai su ka canza daga tilo zuwa jam'i. Idan ka na so ka faɗi launin wani abu da Turanci, za ka fara kawo sunan launin - sannan sai ka kawo sunan abun da ka ke so ka faɗi launin sa. Ga wasu misalai a kan yadda ake amfani da launuka a Turanci.


Misali:

    1. I have a white cap. (Ina da farar hula)
    2. He bought a black T-shirt. (Ya siyo baƙar T-shirt)
    3. She wears red glasses. (Ta kan sa jajayen tabarau)
    4. They sat on black armchairs. (Sun zauna a baƙaƙen kujeru)
    5. We live in a green house. (Mu na rayuwa a koren gida)


Ina ga za mu dakata a nan. Amma kafin nan ya na da kyau a sani cewa a Turanci launuka ba su da jinsi, kuma babu bambanci tsakanin tilo da jam'i. Sannan launuka su kan zo ne kafin sunan da su ke bayyana launin sa. Ga duk wanda ya ke da tambaya, ya na iya rubuta ta a wajen comment da ke ƙasa. Za mu amsa masa, idan Allah ya sa mun sani.


Ka da ku manta, ku na iya gayyato abokan ku zuwa shafin nan domin ƙaruwa da darusan da mu ke wallafawa a shafin nan. Mu na godiya da ziyarartar shafin nan da ku ke.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post