Wasu kalmomi da ake amfani da su a maimakon kalmar BEAUTIFUL

Assalamu alaikum, masu bibiyar wannan shafi na koyan Turanci. Muna fatan kuna fa'idantuwa da darusan da kuke karantawa a wannan shafi. Kamar ko da yaushe, a wannan darasi ma mun zo muku da wani bayani mai matuƙar amfani. Darasin nan da zamu yi, zamu yi bayani ne game da wasu kalmomi da zaku iya amfani da su a maimakon kalmar beautiful.



A baya-bayan nan, mun wallafa wani darasi makamancin wannan. Wato darasin da acikinsa muka jero wasu kalmomi kusan guda biyar da zaku iya amfani dasu a maimakon kalmar good. Sai dai a wannan darasi da kuke karantawa, zamu kawo muku wasu kalmomin ne da zaku iya amfani dasu a maimakon kalmar beautiful. Amma kafin sannan, zamu fara da bayanin mece ce ma'anar kalmar beautiful - daga bisani misalai su biyo baya.


Gwarancine rashin yin amfani da kalma a bisa muhallin da yadace da ita acikin kowace irin al'umma ce. Domin kowace al'umma akwai muhallin da take aza kowace kalma a cikin jimla.


Shin ko kun san yadda tambaya da Turanci?

Me kalmar BEAUTIFUL take nufi?

Da turanci, idan aka ce beautiful, ana nufin: kyakkyawa ko wani abu mai kyau. Misali, kamar mutum ya ce: a beautiful house, ko a beautiful baby. Wannan kalma akan yi amfani da ita ne domin bayyana kyawun mace ko wata dabba ko wani abu maras rai. Bari mu dubi waɗannan misalai dake tafe mu gani:


Shin ko kun san yadda ake amfani da kalmar WOULD?

    1. I passed by a beautiful hotel. (Na wuce ta kusa da wani kyakkyawan otal)
    2. Some children are playing in a beautiful garden. (Ƙananun yaran suna wasa a wani kyakkyawan lambu)
    3. She has grown some beautiful flowers in her garden. (Ta shuka kyawawan fulawoyi a lambunta)
    4. We saw a beautiful electric car. (Mun ga wata kyakkyawar mota mai aiki da lantarki)
    5. They wandered the most beautiful places in the country. (Sun yawata gurare mafiya kyau a ƙasar)


Idan muka dubi waɗannan misalai zamu ga cewa kalmar beautiful tazo a gurare dadama kuma ta bayyana kyawun ababen da ake magana akansu. To duk inda kalmar beautiful tazo muna iya sauyata da ɗaya daga cikin kalmomin nan dake tafe a ƙasa, ba tare da canzuwar ma'ana ba.


Kalmomin sune:

    1. Amazing
    2. Awesome
    3. Beautiful
    4. Bewitching
    5. Brilliant
    6. Enchanting


Shin ko kun san yadda zaku bayyana yanayi da Turanci?

Bari mu buga misali guda ɗaya da kalmar beautiful. Daga bisani mu sauya kalmar beautiful da ɗaya daga cikin kalmomi guda biyar dake sama:


  • She has a beautiful garden. (Tana da lambu mai kyau)


Idan muka cire kalmar beautiful a misalin nan na sama, muka sa ɗaya daga cikin waɗancan kalmomi biyar dake sama, zamu ga duk ma'ana ɗaya suke bayarwa.


    1. She has an amazing garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)
    2. She has an awesome garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)
    3. She has a bewitching garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)
    4. She has a brilliant garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)
    5. She has an enchanting garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)


Abin lura da waɗannan kalmomin shine, su waɗannan kalmomin suna nuna matuƙar kyau ne. Wato idan kace beautiful, yana nufin kyakkyawa ko mai kyau. Amma idan ka ɗakko ɗaya daga cikin waɗancan kalmomi biyar ɗin sama zasu baka ma'anar kyakkyawan gaske ko kyakkyawa sosai ko mai matuƙar kyau. Haka kuma, kana iya cewa very beautiful. Amma ba zayyiwu kayi amfani da kalmar very tare da ɗaya daga cikin waɗancan kalmomi biyar ɗin dake sama ba.


Misali, kana iya cewa:


  • She has a very beautiful garden. (Tana da lambu mai kyau sosai)

Amma, ba zayyiwu kace:


  • She has a very amazing garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)

Hakama, ba zayyiwu kace:


  • She has a very awesome garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)

Hakama dai, ba zayyiwu kace:


  • She has a very bewitching garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)

Sannan, ba zayyiwu kace:


  • She has a very brilliant garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)

Haka kuma, ba zayyiwu kace:


  • She has a very enchanting garden. (Tana da lambu mai matuƙar kyau)


Shin ko kun san ta yadda zaku fara koyan Turanci?

Faɗin haka gwaranci ne a harshen Turanci. Domin waɗannan kalmomin ba a nuna matuka ko gayarsu da kalmar very. Maimakon haka, akwai wasu kalmomi da ake amfani dasu domin nuna gaya ko matukar irin waɗancan kalmomi biyar ɗin. Kalmomin sune: absolutely, certainly, extremely, really, quite da sauransu.


Bari mu ɗauki waɗannan kalmomi, mu yi amfani dasu a waɗannan misalai dake tafe. Misali:


    1. Her garden is extremely amazing. (Lambunta yana da matuƙar kyau)
    2. Her garden is extremely brilliant. (Lambunta yana da matuƙar kyau)
    3. Her garden is extremely awesome. (Lambunta yana da matuƙar kyau)


Duk inda kalmar extremely tazo a waɗannan misalai uku na sama - za a iya canzata da ɗaya daga cikin ire-irenta, wato su: absolutely, certainly, really da sauransu.


Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da launuka da Turanci?

Babu mamaki a samu wasu kalmomin dake da ma'ana irinta da beautiful waɗanda watakila basa daga cikin kalmomi biyar da muka lissafo a sama. To yana da kyau, idan anci karo dasu, a fahimci yadda ake amfani dasu a jimla. Gwarancine rashin yin amfani da kalma a bisa muhallin da ya dace da ita acikin kowace irin al'umma ce. Domin kowace al'umma akwai muhallin da take aza kalmominta a cikin jimla.


Muna masu rufe wannan darasi da waiwaye adon tafiya, wanda shine bambance wace kalmace ake amfani da ita tare da very da kuma waɗanda ba a amfani dasu tare da very. Sannan kuma, su waɗancan kalmomin guda biyar suna nuna matuƙar kyau fiye da yadda kalmar beautiful take nunawa. Bayanai game da yadda ake amfani da waɗannan kalmomi sun gabata a sama tare misalai.


Zamu dakata anan muna fatan Allah yasa a amfana da abubuwan da ake karantawa. Mun gode sai wani lokaci.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post