Yadda ake rubuta sunan Ƙasashen Duniya da Turanci

Masu bibiyar wannan shafi na koyan Turanci, Assalamu alaikum. Barkanmu da warhaka, da kuma kasancewa a wani darasi, wanda a cikinsa za muyi bayani dalla-dalla game da yadda ake rubuta sunan kowace ƙasa daga cikin ƙasashen duniya. Idan ka na karanta littattafan Turanci ko jaridun Turanci, za kaga wani lokaci akan rubuta sunan wata ƙasa tare da definite article (wato tare da kalmar the). Misali, kamar: the Philippines da the United States. Amma wasu ƙasashen kuma akan rubuta sunayensu ba tare da definite article ba. Misali, kamar: France da Germany da Honduras.

    1. He would like to study Accounting at the university of Manila in the Philippines.
    2. She would like to study Spanish Literature at the university of Seville in Spain.


Idan muka dubi waɗannan misalai dake sama sannan kuma muka lura sosai za muga cewa, a misali na farko kafin sunan Philippines mun rubuta kalmar the, amma a misali na biyu kafin sunan ƙasar Spain ba mu rubuta kalmar the ba.

Mutane dadama kama daga ɗalibai da waɗanda suke koyan Turanci - sukan tafka wasu kurakurai wajen rubuta sunayen wasu ƙasashen duniya. Domin wasu ƙasashen akan rubuta sunayensu tare da definite article, wasu kuma ba tare da shi ba, kamar dai yadda bayani ya gabata a sama. Rashin rubuta wannan kalma tare da sunan ƙasar da ake rubuta sunanta da ita, yakan jawo asarar maki a jarabawar Turancin English. Rubuta wannan kalma tare da sunan ƙasar da ba arubuta shi da ita, shima yakan jawo asarar maki.


Kafin mu tsunduma cikin darasin, idan ba ku-yi subscribe na channel ɗin mu ba, ku-yi ƙoƙari, ku-je YouTube, ku-binciko Arewapot, ku-yi subscribe ɗinta. Saboda yin haka zai ba ku damar samun saƙwannin imel a duk lokacin da muka yi sabon darasi.


Karanta cikakken bayanin

A ƙa'idar Turanci kowace ƙasa daga cikin ƙasashen duniya idan za arubuta sunanta, to sunan nata kaɗai ake rubutawa, ba tare da saka definite article ɗin ba. Misali, Brazil ake rubutawa ba the Brazil ba, Cambodia ake rubutawa ba the Cambodia ba, Oman ake rubutawa ba the Oman ba, Nigeria ake rubutawa ba the Nigeria ba da dai sauransu.


Sai dai kuma kaman yadda mu kayi misali a can sama, mun ce akwai wasu ƙasashe kaɗan waɗanda ba asaka musu definite article idan za a rubuta sunayensu. Irin waɗannan ƙasashen ƙasashe ne da aka samar dasu ko kuma suka samu ta hanyar haɗa wasu yankuna daban-daban masu zaman kansu waje ɗaya, sannan aka samar da su.


Irin waɗannan ƙasashen kaɗai ake rubuta sunayensu tare da definite article da Turanci. Jerin sunayen waɗannan ƙasashen shi ne:

    1. the Bahamas
    2. the Fiji
    3. the Netherlands
    4. the Philippines
    5. the United Arab Emirates (UAE)
    6. the United Kingdom (UK)
    7. the United States (US)


Ga misalan yadda ake rubuta sunayen waɗannan ƙasashen a cikin jimloli:

    1. These pairs of shoes were made in the United Kingdom. (Waɗannan takalman anhaɗasu ne a Burtaniya)
    2. There are many Islands in the Bahamas. (Akwai tsibirai dayawa a Bahamas)
    3. They lived in the Philippines for 25 years. (Sun zauna a Filifins na tsawon shekaru 25)
    4. Android and iPhone were invented in the United States. (Android da iPhone anƙirƙirosu ne a Amurka)
    5. The tallest building in the world is in the United Arab Emirates. (Ginin dayafi kowane gini tsawo a duniya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa yake)


Akan taƙaita sunayen wasu daga cikin waɗannan ƙasashe, the United Arab Emirates zuwa the UAE; the United Kingdom zuwa the UK; the United States zuwa the US. Yana dakyau asani cewa ba duk ƙasashen da aka samar dasu ta hanyar haɗa wasu yankuna daban-daban zuwa waje ɗaya bane ake rubuta sunayensu tare da definite article ba.


Sannan kuma, idan ɗaya daga cikin ƙasashen da ake rubuta sunayensu tare da definite article tana da wani suna na daban, wancan sunan na daban ɗin idan za arubuta shi ba arubuta shi tare da definite article. Misali, the United States tana da wani suna wato America. Idan za ayi amfani da America a maimakon the United States, ba arubuta definite article.

    1. the Netherlands (Holland)
    2. the United Kingdom (Britain)
    3. the United States (America)


Misali:

    1. He wants to visit Britain. (Yana so ya ziyarci Burtaniya)
    2. She wants to travel to Holland. (Tana so ta tafi Holland)


Sannan kuma na taɓa jin wani jawabi na darusan Turanci, wanda a cikin sa aka ce akwai wasu ƙasashen da suma yakamata ake rubuta sunansa tare da definite article duk da cewa su ba yankuna daban-daban aka tattara aka samar dasu ba. Waɗannan ƙasashen su ne: Burkina Faso da D.R. Congo da Gambia da kuma Sudan.


Sauran ƙasashen kuma duk ba arubuta sunayensu tare da definite article. Sunan nasu kaɗai ake rubutawa. Misali:

    1. Bangladesh ba the Bangladesh ba
    2. Cameroon ba the Cameroon ba
    3. Guatamala ba the Guatamala ba
    4. Pakistan ba the Pakistan ba
    5. Qatar ba the Qatar ba
    6. Russia ba the Russia ba
    7. Uzbekistan ba the Uzbekistan ba


Misali:

    1. These two pairs of jeans were made in Italy. (Waɗannan wandunan jins guda biyun anyisu ne a Italiya)
    2. There are many ancient buildings in Egypt. (Akwai tsofaffin gine-gine dayawa a Misra)
    3. We lived in Portugal for 5 years. (Mun zauna a ƙasar Fortugal na tsawon shekaru biyar)
    4. There are many film industries in India. (Akwai masana'antun fim dayawa a Indiya)
    5. She has been to Oman. (Ta taɓa zuwa ƙasar Oman)


Za mu dakata a nan, da fatan dai ana amfanuwa da darusan koyan Turanci da ake karantawa a shafin nan da kuma waɗanda ake kallo a tashar Arewapot dake YouTube. Idan da mai tambaya sai ya-je ƙasa wajen comment, ya-rubuta. Mu kuma zamu amsa masa, idan Allah yasa mun sani.


Ka da dai ku-manta, ku-je YouTube, ku-yi subscribe tare da taɓa alamar ƙararrawa, domin samun saƙwannin imel a duk lokacin damu ka ɗaura sabon darasi, Mun gode.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post