Assalamu alaikum. Barkan mu da yau masu bibiyar wannan shafi na koyan Turanci. Barkan mu da sake kasancewa a wani sabon darasi wanda a cikin sa za mu kawo sunayen wasu ɓangarori da a ke cikin gari. Idan ka na so ka bayar da labarin wasu gurare da ke cikin gari da ka ziyarta, kuma ba ka san sunayen guraren da Turanci ba, ga jerin sunayen a ƙasa.
Akwai wasu darusa na koyan Turanci da yawa a shafin nan kamar darasin yadda ake rubuta sunayen ƙasashen duniya da sauransu. Kafin mu kawo sunayen waɗannan guraren, ga misalin yadda ake amfani da su a cikin jimla.
Wannan shi ne bayanin yadda ake amfani da waɗannan kalmomin da kuma yadda ake aiki da su. Da fatan a na amfanuwa da darusan da a ke karantawa a shafin nan. Kada a manta a ci gaba da kasancewa da shafin na koyan Turanci a harshen Hausa. Sannan kuma, idan ba ku yi subscribe na channel ɗin mu ba, ku yi ƙoƙari, ku je YouTube, ku binciko Arewapot, ku yi subscribe ɗin ta. Domin yin hakan shi zai ba ku damar samun saƙwannin imel a duk lokacin da mu ka yi sabon darasi.
Misali:
- The people visited the museum. (Mutanen sun ziyarci gidan kayan tarihin)
- The children want to go to the zoo on holiday. (Yaran su na son zuwa hutu gidan namun dajin)
- She goes to the supermarket on weekends. (Ta kan je sufamaket a ƙarshen mako)
- He shops for clothes in the boutique. (Ya kan siyo kayan sawa a kantin siyar da kayan sawa na zamani)
- I will go to the laundry. (Zan je wajen wankin kaya)
- Airport - tashar jirgin sama
- Apartment - gida, masauƙi
- Bakery - magasa
- Bank - banki
- Barn - gidan gona
- Barrack - barikin sojoji
- Beach - bakin teku
- Boutique - shagon siyar da kayan sawa na zamani
- Bureau - ofishi, babban ofishi
- Bus station - tashar bas
- Cafe - shago ko kantin gahawa
- Church - coci, mujami'a
- Cinema - gidan silima, gidan fim
- Clinic - ƙaramin wajen kula da marasa lafiya
- College - kwaleji
- Company - kamfani
- Court - kotu
- Club - kulob, gidan rawa, dandamalin wasa
- Factory - masana'anta, kamfani
- Farm - gona
- Filing station - gidan mai
- Forest - jeji, daji
- Garage - gareji
- Grave - ƙabari, kabari
- Graveyard - maƙabarta
- Grocery - shagon siyar da kayan abinci kamar sukari
- Hospital - asibiti
- Hotel - otal, hotal
- House - gida
- Jungle - daji, ƙungurmin daji
- Laboratory - ɗakin gwaje-gwaje da binciken kimiyya
- Laundry - wajen wanke kaya
- Library - ɗakin karatu
- Mall - babban kantin siyayya
- Market - kasuwa
- Metro - tashar jirgin ƙarƙashin ƙasa
- Mill - wajen da ake niƙa alkama, masara, gero da sauransu
- Mosque - masallaci
- Motor park - tashar mota
- Museum - gidan kayan tarihi
- Office - ofis, ofishi
- Park - lambun hutu
- Pharmacy - wajen bayar da magani
- Police station - ofishin 'yan sanda
- Post office - ofishin akwatin gidan waya
- Power station - gidan nefa
- Prison - gidan yari, gidan kaso, gidan jarin
- Radio station - tashar rediyo
- Railway - tashar jirgin ƙasa
- River - kogi
- School - makaranta
- Station - tasha
- Shop - shago
- Stadium - filin wasan guje-guje da tsalle-tsalle
- Street - anguwa, santa, layi, titi
- Supermarket - sufamaket, babban kantin siyayya
- Temple - mujami'a, ɗakin bauta
- Traffic light - fitilar bada hannu
- University - jami'a
- Workshop - wajen aiki, shagon aiki
- Zoo - gidan namun daji
Wannan shi ne bayanin yadda ake amfani da waɗannan kalmomin da kuma yadda ake aiki da su. Da fatan a na amfanuwa da darusan da a ke karantawa a shafin nan. Kada a manta a ci gaba da kasancewa da shafin na koyan Turanci a harshen Hausa. Sannan kuma, idan ba ku yi subscribe na channel ɗin mu ba, ku yi ƙoƙari, ku je YouTube, ku binciko Arewapot, ku yi subscribe ɗin ta. Domin yin hakan shi zai ba ku damar samun saƙwannin imel a duk lokacin da mu ka yi sabon darasi.