Sunayen Wasu Ɓangarorin Gari Da Turanci

Assalamu alaikum. Barkan mu da yau masu bibiyar wannan shafi na koyan Turanci. Barkan mu da sake kasancewa a wani sabon darasi wanda a cikin sa za mu kawo sunayen wasu ɓangarori da a ke cikin gari. Idan ka na so ka bayar da labarin wasu gurare da ke cikin gari da ka ziyarta, kuma ba ka san sunayen guraren da Turanci ba, ga jerin sunayen a ƙasa.
Akwai wasu darusa na koyan Turanci da yawa a shafin nan kamar darasin yadda ake rubuta sunayen ƙasashen duniya da sauransu. Kafin mu kawo sunayen waɗannan guraren, ga misalin yadda ake amfani da su a cikin jimla.


Misali:

    1. The people visited the museum. (Mutanen sun ziyarci gidan kayan tarihin)
    2. The children want to go to the zoo on holiday. (Yaran su na son zuwa hutu gidan namun dajin)
    3. She goes to the supermarket on weekends. (Ta kan je sufamaket a ƙarshen mako)
    4. He shops for clothes in the boutique. (Ya kan siyo kayan sawa a kantin siyar da kayan sawa na zamani)
    5. I will go to the laundry. (Zan je wajen wankin kaya)


    1. Airport - tashar jirgin sama
    2. Apartment - gida, masauƙi
    3. Bakery - magasa
    4. Bank - banki
    5. Barn - gidan gona
    6. Barrack - barikin sojoji
    7. Beach - bakin teku
    8. Boutique - shagon siyar da kayan sawa na zamani
    9. Bureau - ofishi, babban ofishi
    10. Bus station - tashar bas
    11. Cafe - shago ko kantin gahawa
    12. Church - coci, mujami'a
    13. Cinema - gidan silima, gidan fim
    14. Clinic - ƙaramin wajen kula da marasa lafiya
    15. College - kwaleji
    16. Company - kamfani
    17. Court - kotu
    18. Club - kulob, gidan rawa, dandamalin wasa
    19. Factory - masana'anta, kamfani
    20. Farm - gona
    21. Filing station - gidan mai
    22. Forest - jeji, daji
    23. Garage - gareji
    24. Grave - ƙabari, kabari
    25. Graveyard - maƙabarta
    26. Grocery - shagon siyar da kayan abinci kamar sukari
    27. Hospital - asibiti
    28. Hotel - otal, hotal
    29. House - gida
    30. Jungle - daji, ƙungurmin daji
    31. Laboratory - ɗakin gwaje-gwaje da binciken kimiyya
    32. Laundry - wajen wanke kaya
    33. Library - ɗakin karatu
    34. Mall - babban kantin siyayya
    35. Market - kasuwa
    36. Metro - tashar jirgin ƙarƙashin ƙasa
    37. Mill - wajen da ake niƙa alkama, masara, gero da sauransu
    38. Mosque - masallaci
    39. Motor park - tashar mota
    40. Museum - gidan kayan tarihi
    41. Office - ofis, ofishi
    42. Park - lambun hutu
    43. Pharmacy - wajen bayar da magani
    44. Police station - ofishin 'yan sanda
    45. Post office - ofishin akwatin gidan waya
    46. Power station - gidan nefa
    47. Prison - gidan yari, gidan kaso, gidan jarin
    48. Radio station - tashar rediyo
    49. Railway - tashar jirgin ƙasa
    50. River - kogi
    51. School - makaranta
    52. Station - tasha
    53. Shop - shago
    54. Stadium - filin wasan guje-guje da tsalle-tsalle
    55. Street - anguwa, santa, layi, titi
    56. Supermarket - sufamaket, babban kantin siyayya
    57. Temple - mujami'a, ɗakin bauta
    58. Traffic light - fitilar bada hannu
    59. University - jami'a
    60. Workshop - wajen aiki, shagon aiki
    61. Zoo - gidan namun daji


Wannan shi ne bayanin yadda ake amfani da waɗannan kalmomin da kuma yadda ake aiki da su. Da fatan a na amfanuwa da darusan da a ke karantawa a shafin nan. Kada a manta a ci gaba da kasancewa da shafin na koyan Turanci a harshen Hausa. Sannan kuma, idan ba ku yi subscribe na channel ɗin mu ba, ku yi ƙoƙari, ku je YouTube, ku binciko Arewapot, ku yi subscribe ɗin ta. Domin yin hakan shi zai ba ku damar samun saƙwannin imel a duk lokacin da mu ka yi sabon darasi.
إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم