Assalamu alaikum, jama'ar wannan shafi. Barkan mu da wannan lokaci tare da farin cikin sake kasancewa da ku a wani sabon darasi, wanda a cikin sa za mu yi bayanin wasu sana'o'i tare da masu yin su da Turanci. Wannan darasi ya na daga cikin muhimman darusa da a ke so mai koyan Turanci ya sani tare da haddace kalmomin da ke cikin sa.
A wasu darusa da su ka gabata mun kawo sunayen wasu ɓangarori na gari da kuma bayanin yadda ake amfani da kalmar ENVIOUS OF da kuma PROUD OF, sai kuma darasi a kan yadda ake rubuta sunayen ƙasashen duniya da Turanci. A cikin darasin nan kuma za mu jero wasu sana'o'i tare da sunayen waɗanda su ke yin waɗannan sana'o'in a Turanci da Hausa.
Amma kafin mu kawo sunayen sana'o'in ga wasu misalai da ke tafe ƙunshe da bayanan yadda ake amfani da sana'o'in da masu su yin da Turanci.
Da fatan a na amfanuwa da darusan koyan Turanci da mu ke wallafa a shafin nan. Za mu dakata a nan sai kuma Allah kai mu wani lokaci a gaba mu zo da wani sabon darasi. Ka da dai a manta mu na nan a YouTube da Instagram da Facebook da Twitter domin koyan Turanci cikin harshen Hausa. Mun gode.
Amma kafin mu kawo sunayen sana'o'in ga wasu misalai da ke tafe ƙunshe da bayanan yadda ake amfani da sana'o'in da masu su yin da Turanci.
Misali:
- Cristiano Ronaldo is a footballer. (Cristiano Ronaldo ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne)
- Ali Nuhu is an actor. (Ali Nuhu ɗan wasan kwaikwayo ne)
- Mark Angel is a comedian. (Mark Angel ɗan wasan kwaikwayo ban dariya ne)
- Fatima is an authoress. (Fatima marubuciya ce)
- The journalist discussed with me. (Ɗan jaridar ya tattauna da ni)
- The businesswoman invests in Cryptocurrency. ('Yar kasuwar ta sa hannun jari a kasuwar kirifto)
- The architect drew a magnificent house. (Mai zane-zanen ya zana gida mai matuƙar kyau)
- The cook made a yummy soup. (Kukun ya girka miya mai daɗi sosai)
Yanzu kuma ga jerin sana'o'in tare da sunayen masu yin su a Hausa da Turanci:
- Actor - ɗan wasan kwaikwayo
- Actress - ƴar wasan kwaikwayo
- Comedy - wasan kwaikwayo na ban dariya
- Comedian - ɗan wasan kwaikwayon ban dariya, ƴar wasan kwaikwayon ban dariya
- Dancer - mai yin rawa, ƴar wasan rawa, ɗan rawa, 'yar rawa
- Director - mai bada umarni, shugaba a wata ma'aikata
- Film producer - mai shirya wasan kwaikwayo
- Guitarist - makaɗin jita
- Musician - makaɗi, makaɗiya
- Pianist - makaɗin fiyano
- Singer - mawaƙi, mawaƙiya
- Violinist - makaɗin goge
- Anchorman - mai karanta labarai (namiji)
- Anchorwoman - mai karanta labarai (mace)
- Editor - mai tsara rubutu ko labarai
- Journalism - aikin jarida, harkar jarida
- Journalist - ɗan jarida, ƴar jarida
- Reporter - mai kawo rahoto, ɗan jarida, ƴar jarida
- Television presenter - mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin
- Architecture - ilimin zane-zane, aikin zane-zane
- Architect - mai zane-zane, mai ilimin zane-zane
- Astronomy - ilimin falaki, ilimin zuwa sararin samaniya
- Astronaut - mai ilimin falaki, mai ilimin zuwa sararin samaniya
- Author - marubuci, mawallafi
- Authoress - marubuciya, mawallafiya
- Courier - ɗan aike, mai kai wasiƙa
- Mail carrier - ɗan aike, mai kai wasiƙa
- Postman - ɗan aike, mai kai wasiƙa
- Writer - marubuci, marubuciya
- Writing - rubutu, harkokin rubuce-rubuce
- Baking - gashin buredi ko kek
- Baker - mai gashin buredi ko kek
- Bakery - gidan buredi, magasar buredi ko kek
- Baber - mai aski
- Beautician - mai kwalliya
- Dressmakers - mai haɗa kayan sawa, tela
- Fashion designing - tsara kayan sawa
- Fashion designer - mai tsara kayan sawa
- Graphic designing - tsara hoto
- Graphic designer - mai tsara hoto
- Hairdresser - mai gyaran gashi, mai kwalliyar gashi
- Photography - ɗaukar hoto
- Photographer - mai ɗaukar hoto
- Blogging - harkar yin rubuce-rubuce a intanet
- Blogger - mai yin harkar yin rubuce-rubuce a intanet
- Boxing - damben zamani, dambe
- Boxer - ɗan damben zamani, ƴar damben zamani
- Business - kasuwanci, siya da siyarwa
- Businessman - ɗan kasuwa
- Businesswoman - ƴar kasuwa
- Merchant - ɗan kasuwa, ƴar kasuwa
- Salesperson - ɗan kasuwa, ƴar kasuwa
- Trading - kasuwanci, siya da siyarwa
- Trader - ɗan kasuwa, ƴar kasuwa, mai siya da siyarwa
- Carpentry - aikin kafinta
- Carpenter - kafinta
- Cleaning - mai goge-goge da share-share
- Cooking - girki, sanwa, dafa abinci
- Cook - kuku, mai girki
- Doorman - mai tsaron kofa, mai gadi
- Maid - mai hidima, mai aikace-aikace
- Mason - mai tausa
- Coaching - bayar da horo, koyar da mutane, horas da mutane
- Coach - mai bayar da horo, mai horaswa
- Training - bayar da horo, tirenin
- Trainer - mai bayar da horo, mai horaswa
- Trainee - wanda ake horaswa, wanda a ke wa tirenin
- Doctor - likita
- Dentist - likitan haƙori
- Nurse - mai kula da mara lafiya
- Nutritionist - masanin abinci mai gina jiki
- Optician - likitan ido
- Pharmacist - mai bayar da magani
- Physician - likita, masanin lafiyar jikin ɗan Adam
- Psychiatrist - likitan masu matsalar kai
- Surgeon - likita mai aiki, likitan fiɗa
- Veterinarian - likitan dabbobi
- Drycleaning - sana'ar wanki da guga
- Drycleaner - mai sana'ar wanki da guga
- Electricity - wutar lantarki, wutar nefa
- Electrician - latirishan, mai gyaran lantarki, ruwaya
- Engineering - tsara gine-gine, gyaran kayan lantarki
- Engineer - injiya, mai gyaran kayan lantarki, masanin gine-gine
- Mechanic - bakanike, makanike
- Employer - mai ɗaukar ma'aikata
- Employee - wanda aka ɗauka aiki
- Farming - noma
- Farmer - manomi, manomiya
- Gardening - yin lambu
- Gardener - mai lambu
- Fishing - kamun kifi, su
- Fisherman - masunci, mai kama kifi
- Fisherwoman - masunciya, mai kama kifi (mace)
- Football - kwallon kafa, harkar wasan ƙwallon ƙafa
- Footballer - ɗan wasan ƙwallon ƙafa, ɗan ƙwallo
- Interpreting - aikin fassara
- Interpreter - mai fassara
- Translating - aikin fassara
- Translator - mai fassara
- Labour - aikin ƙwodago, ƙwodago
- Labourer - mai aikin ƙwodago, ɗan ƙwodago
- Mining - haƙan ma'adanai, tono ma'adanai
- Miner - mai haƙan ma'adanai, mai tonon ma'adanai
- Painting - fenti, yin fenti
- Painter - mai fenti
- Plumbing - gyaran hanyar ruwa
- Plumber - mai gyaran hanyar ruwa, filamba
- Politics - siyasa
- Politician - ɗan siyasa, ƴar siyasa
- Welding - sana'ar walda
- Welder - mai walda
- Judge - mai shari'a, alƙali
- Lawyer - lauya
- Prosecutor - mai bincike a kotu
- Librarian - mai zama a ɗakin karatu
- Lecturer - lakcara, malamin jami'a, malamar jami'a
- Professor - farfesa, shehin malami, malamin jami'a, malamar jami'a
- Pupil - ɗalibin firamare, ɗalibar firamare, mai neman ilimi
- Student - ɗalibi, ɗaliba, mai neman ilimi
- Teacher - malami, malama, mai koyar da karatu
- Detective - mai binciken laifi
- Guard - mai gadi, mai tsaro
- Body guard - mai tsaron mutum, mai take baya
- Fire fighter - ma'aikacin kwana-kwana, ma'aikaciyar kwana-kwana
- Policeman - ɗan sanda
- Policewoman - ƴar sanda
- Soldier - soja
- Spy - ɗan leƙen asiri, ƴar leƙen asiri
- Conductor - kwandesta, yaron mota, karen mota
- Driver - matuƙi, direba
- Bus driver - matuƙin motar safa, matuƙin bas
- Taxi driver - matuƙin tassi
- Flight attendant - fasinjojin da za a tafi da su a jirgin sama
- Steward - mai lura da fasinjoji a jirgin sama ko na ruwa (namiji)
- Stewardess - mai lura da fasinsojoji a jirgin sama ko na ruwa (mace)
- Pilot - matuƙin jirgin sama
- Cashier - mai kula da harkokin ƙudi, akawu
- Director - darakta, mai bada umarni
- Manager - shugaba, manaja
- Secretary - sakatare
- Reception - wajen karɓan baki, karɓan baki
- Receptionist - mai karɓan baki
- Waiter - mai kawo abinci a otal (namiji)
- Waitress - mai kawo abinci a otal (mace)
- Athlete - ɗan wasa, ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ɗan wasan motsa jiki, ƴar wasa, ƴar wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ƴar wasan motsa jiki
- Coach - mai bada horo
- Player - ɗan wasa, ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ɗan wasan motsa jiki, ƴar wasa, ƴar wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ƴar wasan motsa jiki
- Trainer - mai bada horo
- Trainee - mai karɓan horo
- Banker - mai aikin banki
- Blacksmith - maƙeri
- Builder - mai gini, magini
- Bricklayer - magini, mai gini
- Butcher - mahauci, barunje, ɗan fawa
- Cobbler - mai gyaran takalma
- Grocer - mai tsaron shagon abinci
- Jeweler - mai siyar da kayan kwalliya
- Locksmith - maƙerin kwaɗo
- Shepherd - makiyayi, mai kiwo
- Shoemaker - baduku, mai haɗa takalma
- Tile-setter - mai sa tayils
- Watchmaker - maƙerin agogo
Da fatan a na amfanuwa da darusan koyan Turanci da mu ke wallafa a shafin nan. Za mu dakata a nan sai kuma Allah kai mu wani lokaci a gaba mu zo da wani sabon darasi. Ka da dai a manta mu na nan a YouTube da Instagram da Facebook da Twitter domin koyan Turanci cikin harshen Hausa. Mun gode.