Yadda ake bayyana yanayi da Turanci

 


Assalamu alaikum, Jama'a. Barkanmu da wannan lokaci da kuma sake kasancewa a wani sabon darasi na koyan Turanci, wanda a cikinsa za mu yi bayanin daki-daki akan yadda ake bayyana yanayi da Turanci. Wato kamar yadda za ka ce "yau ana rana sosai" ko "yau ana sanyi" ko kuma "yau ana hazo" da dai sauransu.



Fahimtar yadda ake bayyana yanayi abun ne mai matuƙar muhimmanci ga ɗalibai da sauran masu sha'awar koyan Turanci. Saboda ta na iya kasancewa wani lokaci za ka buƙaci bayyana yanayi a sa'adda da ka ke hira da wani cikin harshen Turanci ko kuma wani zai tambayeka ka-bayyana masa yanayi da Turanci. To ka ga idan ka san yadda ake bayyanawa, sai dai ya ji ka fara bayani.


Da farkon fari kafin mu nitsa cikin darasin ga jerin wasu kalmomi da ake amfani da su wajen bayyana yanayi:


Kalma ta farko itace:

Rain wato Ruwan sama. Rainy kuma yanayin Ruwan sama.


Kalma ta biyu itace:

Sun wato Rana. Sunny kuma yanayin zafin Rana.


Kalma ta uku itace:

Haze wato Hazo ko Buji. Hazy kuma yanayin Hazo ko Buji.


Kalma ta huɗu itace:

Wind wato Iska. Windy kuma yanayin Iska.


Kalma ta biyar itace:

Cloud wato Giza-gizai. Cloudy kuma yanayin Giza-gizai.


Kalma ta shida itace:

Dust wato Ƙura. Dusty kuma yanayin Ƙura.


Kalma ta bakwai itace:

Cool wato Sanyi. Haka nan ma Cool yanayin Sanyi.


Kalma ta takwas itace:

Hot wato Zafi haka kuma wannan kalmar ta nufin yanayin zafi.


Kalma ta tara itace:

Warm wato Zafi haka kuma wannan kalmar ta nufin yanayin zafi.



Kafin mu cigaba da bayani idan wannan shine zuwanka na farko wannan shafi ya na da kyau ka je tasharmu dake YouTube mai suna Arewapot ka-yi subscribe tare da taɓa alamar ƙararrawa. Domin yin hakan shi zai baka damar samun saƙon imel a duk lokacin da mu ka yi sabon darasi a wannan tasha. Mun gode.


Bari mu dawo cikin darasin mu cigaba daga wajen da mu ka tsaya. 


Idan za ka bayyana yanayin Yau, sai ka ce:

It is ... sai ka faɗi yanayin sannan ka kawo kalmar Today daga ƙarshe.


Idan kuma za ka bayyana yanayin Jiya ne, sai ka ce:

It was ... sai ka faɗi yanayin sannan ka kawo kalmar Yesterday a ƙarshe.


Idan kuma za ka yi hasashen yanayin Gobe ne, sai ka ce:

It will be ... sai ka faɗi yanayin sannan ka kawo kalmar Tomorrow a ƙarshe.


Bari mu kawo wasu misalai akan yadda ake amfani da waɗannan kalmomi:


It is cool in winter. (A lokacin hunturu sanyi ake yi)


It is rainy in spring. (A damuna ana yawan yin ruwan sama)


It is windy today. (Yau akwai iska ko kuma Yau ana iska)


It was sunny yesterday. (Jiya anyi rana)


It was rainy on Friday. (Ranar Juma'a anyi ruwan sama)


It was so hazy last week. (Satin da-yawuce anyi hazo sosai)


It will be rainy tomorrow by the grace of God. (Gobe za a yi rana da yaddar Allah)


Wannan shine bayanin yadda ake bayyana yanayi tare da kalmomin da ake amfani da Turanci. Idan da mai tambaya, sai ya je ƙasa wajen comment ya rubuta. Haka kuma kar amanta aje channel ɗinmu dake YouTube ayi subscribe tare da taɓa alamar ƙararrawa. Mun gode.

 


إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم