Assalamu alaikum, jama'a masu bibiyarmu a wannan shafi. Ina mana barkanmu da warhaka tare da farin cikin sake kasancewa daku a wani sabon darasi wanda a cikinsa zamu yi bayanin yadda ake amfani da wasu kalmomin preposition tare da intanet da na'ura mai ƙwaƙwalwa da kuma kafafen yaɗa labarai. Darasin nan na ɗauke da bayanai tare da misalai ga masu koyan turanci da ɗalibai da waɗanda suke bukatar inganta turancinsu. Sau dayawa nakan yi karo da wasu kurakurai waɗanda mutane suke yi wajen nuna wani aiki da suka yi a intanet. Maimakon suyi amfani da kalmar ON, sai kaga sun yi amfani da kalmar IN wanda hakan kuma kuskure ne matuƙa. Irin waɗannan kurakurai hatta waɗanda suka fara ƙwarewa a turanci sukan yisu.
Bawai tare da intanet kaɗai ba hatta sunan computer, wayoyi, gidajen talabijin da rediyo akan yi amfani da wannan kalma ta preposition. Bari mu ga wasu daga cikin irin waɗannan kurakurai a jimlolin dake tafe. Idan mutum yana so ya nunama cewa "yakan saurari labaran BBC Hausa a rediyo", sai kaji yace:
- I listen to BBC Hausa news with my radio.
- I listen to BBC Hausa news in my radio.
Idan muka dubi waɗannan misalai biyu dake sama, zamu iya fahimtar abun da mai magana yake son cewa. Sai dai a ƙa'idar turanci yin hakan kuskure ne. Domin kalmomin WITH da IN anyi amfani da su a muhallin da banasu bane, muhallin kalmar ON ne. Ma'ana sai dai mutum ya ce:
- I listen to BBC Hausa news on my radio.
Wasu daga cikin irin waɗannan kurakuran sune:
- I watched the film in Nexflix. (Na kalli fim ɗin a shafin Nexflix)
- Maryam listens to new songs in Spotify. (Maryam takan saurari sabbi waƙoƙi a manhajar Spotify)
- We have read the news in CRI Hausa website. (Mun karanta labaran a shafin CRI Hausa)
- Many students watch tutorial videos in YouTube. (Ɗalibai dadama sukan kalli bidiyoyin tutorial a YouTube)
Idan mai karatu ya nutsu, ya koma can sama, ya dubi bayanan da mukayi kafin mukawo waɗannan misalai dake sama, shi da kansa zai fahimci dalilin da yasa ba za'ayi amfani da kalmar IN a wajen ba - domin wajen ba muhallinta bane. Saboda haka a duk inda muka ga kalmar IN sai mu gogeta, sannan mu rubuta kalmar ON a wajen, kamar yadda yake a misalan dake tafe:
Ga yadda misalan zasu kasance bayan anyi amfani kalmar da tadace a muhallinta:
- I watched the film on Nexflix. (Na kalli fim ɗin a shafin Nexflix)
- Maryam listens to new songs on Spotify. (Maryam takan saurari sabbi waƙoƙi a manhajar Spotify)
- We have read the news on CRI Hausa website. (Mun karanta labaran a shafin CRI Hausa)
- Many students watch tutorial videos on YouTube. (Ɗalibai dadama sukan kalli bidiyoyin tutorial a YouTube)
Ga misalai tafe domin ƙarin bayani:
- We watch comedy on Facebook. (Mu kan kalli bidiyoyin ban dariya a Facebook)
- She prefers watching on Instagram to Facebook. (Ta fi son yin kallo a Instagram fiye da a Facebook)
- Did you upload some videos on TikTok yesterday? (Shin jiya ka ɗaura wasu bidiyoyi a TikTok?)
Wasu kurakuran kuma wajen bayar da labarin kallon talabijin yake faruwa. Za ji idan mutum ya na son cewa na ga labarai a talabijin ko kuma ya ga wani fim a talabijin za ka ji ya ce: Alhali kuma a ingantaccen turanci, kamata ya yi ya ce:
- I don't watch news regularly on television. (Ban cika kallon labarai a talabijin ba)
- She listens to the program on her radio. (Ta kan saurari shirin a rediyonta)
- They will broadcast the programme on radio. (Za su kawo shirin a rediyo)
Sai kuma masu amfani da wayoyi ko computer. A duk lokacin da za ka cewa ka na da wani abu a cikin wayarka ko computer, za ka yi amfani da ON ne kaɗai.
- Do you have my email address on your phone? (Shin kana da adreshin imel ɗina a wayarka?)
- Yes, I do. (Eh, ina da shi)
- No, I don't. (A'a, bani da shi)
- She saves her photos on my phone. (Takan ajiye hotunanta a wayata)
- I meet new friends on Facebook. (Na kan haɗu da sabbin abokai a Facebook)
- He listens to BBC Hausa news on his phone. (Ya kan saurari labaran BBC Hausa a wayarsa)
Wannan shine bayanin yadda ake aiki da ON tare da internet, computer, television da rediyo. Za mu dakata a nan da fatan a jin daɗin kasancewa da wannan shafi. Ku na iya gayyato mana abokanku da sauran 'yan uwa domin su zo su amfana da darusan koyan turanci da mu ke wallafawa a shafin nan. Fatan za a huta lafiya. Mun gode.