Yadda a ke amfani da kalmomin ENVIOUS OF da PROUD OF

Jama'a masu bibiyar shafin nan; Assalamu alaikum. Barkan mu da warhaka da kuma sake kasancewa a wani sabon darasi, wanda a cikin sa za mu yi bayani game da yadda a ke aiki da kalmar ENVIOUS OF da kuma kalmar PROUD OF. Waɗannan kalmomin sanin su ya na da matuƙar mahimmanci ga duk ɗalibi da kuma sauran masu buƙatar koyan Turanci.
Waɗannan kalmomin, kalmomi ne na adjective da mutane kan so yin amfani da su musamman wajen yin magana da Turanci. A darasin da ya gabata mun yi bayanin yadda ake rubuta sunayen ƙasashen duniya da Turanci. Idan ba ku karanta darasin ba, ku na iya duba cikin darusan da su ka wuce, domin karanta darasin. Bari mu fara da bayanin kalmar Envious of.


ENVIOUS OF

Kalmar envious of ta na nufin yin baƙin cikin da wani ko yi wa hassada da bisa wani abu da ya samu. Misali, kamar ka ce: wane ya na baƙin cikin da wane, ko wane ya na yiwa wane hassada. Mutane da dama su kan so su faɗi haka da Turanci, amma ba su san ya za su ce ba.


To a cikin darasin nan mu na tafe da bayanai tare da misalai a kan yadda a ke cewa wane ya na hassada da wane da Turanci. Amma kafin nan bari mu fara da nuna misalan yadda ake aiki da wannan kalma:
    1. I am envious of ... (Ina hassada da ...)
    2. You are envious of ... (Ki na hassada da..., ka na hassada da ..., ku na hassada da ...)
    3. He is envious of ... (Ya na hassada da ...)
    4. She is envious of ... (Ta na hassada da ...)
    5. We are envious of ... (Mu na hassada da ...)
    6. They are envious of ... (Su na hassada da ...)


Bayan nuna yadda ake amfani da wannan kalma, yanzu kuma ga misalai a kan yadda ake aiki da wannan kalma a cikin jimla.


Misali:

    1. They are very envious of our new apartment. (Su na hassada sosai da sabon masauƙin mu)
    2. We are envious of her traveling to Europe. (Mu na hassada da tafiyar da zuwa Turai)
    3. The people are envious of their neighbours. (Mutanen su na hassada da makwabtan su)
    4. He is envious of her fiancé. (Ya na baƙin ciki da wanda za ta aura)
    5. The brands are envious of their competitors. (Kamfanonin su na hassada da abokan hamayyar su)
Ga kuma bayani tare da misalai a kan yadda a ke kishiyanta ko ƙalubalantar wannan kalma. Wato yadda za a ce wane ba ya hassada da wane.


NOT ENVIOUS OF

Idan kuma za ka ce: wane ba ya hassada da wane ko wani abu da wani ya samu, sai ka sa kalmar not kafin kalmar envious of ɗin. Ga misalai na tafe:
    1. I am not envious of ... (Ba na hassada da ...)
    2. You are not envious of ... (Ba kya hassada da..., ba ka hassada da ..., ba kwa hassada da ...)
    3. He is not envious of ... (Ba ya hassada da ...)
    4. She is not envious of ... (Ba ta hassada da ...)
    5. We are not envious of ... (Ba ma hassada da ...)
    6. They are not envious of ... (Ba sa hassada da ...)


Bayan mun nuna yadda ake ƙalubalanta ko kishiyantar wannan kalmar, yanzu kuma ga cikakkun misalai a cikin jumlolin da ke tafe.


Misali:

    1. They are not very envious of our new apartment. (Ba sa hassada sosai da sabon masauƙin mu)
    2. We are not envious of her traveling to Europe. (Ba ma hassada da tafiyar da zuwa Turai)
    3. The people are not envious of their neighbours. (Mutanen ba sa hassada da makwabtan su)
    4. He is not envious of her fiancé. (Ba ya baƙin ciki da wanda za ta aura)
    5. The brand is not envious of its competitors. (Kamfanonin ba ya hassada da abokan hamayyar sa)
Wannan shi ne bayani tare da misalai a kan yadda ake amfani da wannan. Yanzu kuma ga bayanin kalma ta biyun:


PROUD OF

Proud of kalma ce da a ke amfani da ita kamar yadda ake amfani da kalmar Envious of. Sai dai ma'anonin su sun bambanta. Kalmar Proud of ta na nufin yin alfahari da wani ko wani abu. Kamar ka ce: wane ya na alfahari da kaza ko kaza-kaza. Misali, Aliyu ya na alfahari da iyayen sa.


Kafin mu yi nisa a cikin darasin, ga yadda ake amfani da wannan kalmar tare da wakilan suna na Turanci:
    1. I am proud of ... (
    2. Ina alfahari da ...)
    3. You are proud of ... (Ki na alfahari da..., ka na alfahari da ..., ku na alfahari da ...)
    4. He is proud of ... (Ya na alfahari da ...)
    5. She is proud of ... (Ta na alfahari da ...)
    6. We are proud of ... (Mu na alfahari da ...)
    7. They are proud of ... (Su na alfahari da ...)


Bayan nuna yadda ake amfani da wannan kalma, yanzu kuma ga misalai a kan yadda ake aiki da ita a cikin jimla.


Misali:

    1. I am proud of my new iPhone. (Ina alfahari da sabuwar iPhone ɗina)
    2. He is proud of his nation. (Ya na alfahari da ƙasar sa)
    3. The cook is always proud of his cooking. (Kukun ya kan yi alfahari da girkin sa a ko da yaushe)
    4. The team is proud of its players. (Kungiyar ta na alfahari da 'yan wasan ta)
    5. We are proud of our parents. (Mu na alfahari da iyayen mu)
Ga kuma bayani tare da misalai a kan yadda a ke kishiyanta ko ƙalubalantar wannan kalma. Wato yadda za a ce wane ba ya alfahari da kaza ko kaza-kaza.


NOT PROUD OF

Idan kuma za a ƙalubalanci ko kishiyantar kalmar proud of a kan sa kamar not kafin ta. Wato idan za a ce wane ba ya alfahari da kaza ko kaza-kaza. Misali, kamar a ce: yaron ba ya alfahari da iyayen sa.


    1. I am not proud of ... (Ba na alfahari da ...)
    2. You are not proud of ... (Ba kya alfahari da ..., ba ka alfahari da ..., ba kwa alfahari da ...)
    3. He is not proud of ... (Ba ya alfahari da ...)
    4. She is not proud of ... (Ba ta alfahari da ...)
    5. They are not proud of ... (Ba sa alfahari da ...)
    6. We are not proud of ... (Ba ma alfahari da ...)


Bayan nuna yadda ake kishiyantar wannan kalma a takaice, yanzu kuma ga cikakkun misalai a kan yadda ake kishiyantar wannan kalma a cikin jumloli da ke tafe.


Misali:

    1. I am not proud of my new iPhone. (Ba na alfahari da sabuwar iPhone ɗina)
    2. He is not proud of his nation. (Ba ya alfahari da ƙasar sa)
    3. The cook is not always proud of his cooking. (Kukun ba ya alfahari da girkin sa a ko da yaushe)
    4. The team is not proud of its players. (Kungiyar ba ta alfahari da 'yan wasan ta)
    5. We are not proud of our wealth. (Ba ma alfahari da dukiyar mu)
Wannan shi ne bayani da kuma misalai a kan yadda ake amfani da waɗannan kalmomin. Idan da mai tambaya sai ya rubuta tambayar sa a wajen rubuta comment da ke ƙasa. Za mu amsa masa, idan Allah ya sa mun sani. Sannan ku na iya gayyato abokan ku zuwa shafin nan domin mu ƙaru da juna. Mun gode.
إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم