Wasu sana'o'i da masu yin su da Turanci

Assalamu alaikum, jama'ar wannan shafi. Barkan mu da wannan lokaci tare da farin cikin sake kasancewa da ku a wani sabon darasi, wanda a cikin sa za mu yi bayanin wasu sana'o'i tare da masu yin su da Turanci. Wannan darasi ya na daga cikin muhimman darusa da a ke so mai koyan Turanci ya sani tare da haddace kalmomin da ke cikin sa.
A wasu darusa da su ka gabata mun kawo sunayen wasu ɓangarori na gari da kuma bayanin yadda ake amfani da kalmar ENVIOUS OF da kuma PROUD OF, sai kuma darasi a kan yadda ake rubuta sunayen ƙasashen duniya da Turanci. A cikin darasin nan kuma za mu jero wasu sana'o'i tare da sunayen waɗanda su ke yin waɗannan sana'o'in a Turanci da Hausa.


Amma kafin mu kawo sunayen sana'o'in ga wasu misalai da ke tafe ƙunshe da bayanan yadda ake amfani da sana'o'in da masu su yin da Turanci.


Misali:

    1. Cristiano Ronaldo is a footballer. (Cristiano Ronaldo ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne)
    2. Ali Nuhu is an actor. (Ali Nuhu ɗan wasan kwaikwayo ne)
    3. Mark Angel is a comedian. (Mark Angel ɗan wasan kwaikwayo ban dariya ne)
    4. Fatima is an authoress. (Fatima marubuciya ce)
    5. The journalist discussed with me. (Ɗan jaridar ya tattauna da ni)
    6. The businesswoman invests in Cryptocurrency. ('Yar kasuwar ta sa hannun jari a kasuwar kirifto)
    7. The architect drew a magnificent house. (Mai zane-zanen ya zana gida mai matuƙar kyau)
    8. The cook made a yummy soup. (Kukun ya girka miya mai daɗi sosai)


Yanzu kuma ga jerin sana'o'in tare da sunayen masu yin su a Hausa da Turanci:

    1. Actor - ɗan wasan kwaikwayo
    2. Actress - ƴar wasan kwaikwayo
    3. Comedy - wasan kwaikwayo na ban dariya
    4. Comedian - ɗan wasan kwaikwayon ban dariya, ƴar wasan kwaikwayon ban dariya
    5. Dancer - mai yin rawa, ƴar wasan rawa, ɗan rawa, 'yar rawa
    6. Director - mai bada umarni, shugaba a wata ma'aikata
    7. Film producer - mai shirya wasan kwaikwayo
    8. Guitarist - makaɗin jita
    9. Musician - makaɗi, makaɗiya
    10. Pianist - makaɗin fiyano
    11. Singer - mawaƙi, mawaƙiya
    12. Violinist - makaɗin goge
    13. Anchorman - mai karanta labarai (namiji)
    14. Anchorwoman - mai karanta labarai (mace)
    15. Editor - mai tsara rubutu ko labarai
    16. Journalism - aikin jarida, harkar jarida
    17. Journalist - ɗan jarida, ƴar jarida
    18. Reporter - mai kawo rahoto, ɗan jarida, ƴar jarida
    19. Television presenter - mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin
    20. Architecture - ilimin zane-zane, aikin zane-zane
    21. Architect - mai zane-zane, mai ilimin zane-zane
    22. Astronomy - ilimin falaki, ilimin zuwa sararin samaniya
    23. Astronaut - mai ilimin falaki, mai ilimin zuwa sararin samaniya
    24. Author - marubuci, mawallafi
    25. Authoress - marubuciya, mawallafiya
    26. Courier - ɗan aike, mai kai wasiƙa
    27. Mail carrier - ɗan aike, mai kai wasiƙa
    28. Postman - ɗan aike, mai kai wasiƙa
    29. Writer - marubuci, marubuciya
    30. Writing - rubutu, harkokin rubuce-rubuce
    31. Baking - gashin buredi ko kek
    32. Baker - mai gashin buredi ko kek
    33. Bakery - gidan buredi, magasar buredi ko kek
    34. Baber - mai aski
    35. Beautician - mai kwalliya
    36. Dressmakers - mai haɗa kayan sawa, tela
    37. Fashion designing - tsara kayan sawa
    38. Fashion designer - mai tsara kayan sawa
    39. Graphic designing - tsara hoto
    40. Graphic designer - mai tsara hoto
    41. Hairdresser - mai gyaran gashi, mai kwalliyar gashi
    42. Photography - ɗaukar hoto
    43. Photographer - mai ɗaukar hoto
    44. Blogging - harkar yin rubuce-rubuce a intanet
    45. Blogger - mai yin harkar yin rubuce-rubuce a intanet
    46. Boxing - damben zamani, dambe
    47. Boxer - ɗan damben zamani, ƴar damben zamani
    48. Business - kasuwanci, siya da siyarwa
    49. Businessman - ɗan kasuwa
    50. Businesswoman - ƴar kasuwa
    51. Merchant - ɗan kasuwa, ƴar kasuwa
    52. Salesperson - ɗan kasuwa, ƴar kasuwa
    53. Trading - kasuwanci, siya da siyarwa
    54. Trader - ɗan kasuwa, ƴar kasuwa, mai siya da siyarwa
    55. Carpentry - aikin kafinta
    56. Carpenter - kafinta
    57. Cleaning - mai goge-goge da share-share
    58. Cooking - girki, sanwa, dafa abinci
    59. Cook - kuku, mai girki
    60. Doorman - mai tsaron kofa, mai gadi
    61. Maid - mai hidima, mai aikace-aikace
    62. Mason - mai tausa
    63. Coaching - bayar da horo, koyar da mutane, horas da mutane
    64. Coach - mai bayar da horo, mai horaswa
    65. Training - bayar da horo, tirenin
    66. Trainer - mai bayar da horo, mai horaswa
    67. Trainee - wanda ake horaswa, wanda a ke wa tirenin
    68. Doctor - likita
    69. Dentist - likitan haƙori
    70. Nurse - mai kula da mara lafiya
    71. Nutritionist - masanin abinci mai gina jiki
    72. Optician - likitan ido
    73. Pharmacist - mai bayar da magani
    74. Physician - likita, masanin lafiyar jikin ɗan Adam
    75. Psychiatrist - likitan masu matsalar kai
    76. Surgeon - likita mai aiki, likitan fiɗa
    77. Veterinarian - likitan dabbobi
    78. Drycleaning - sana'ar wanki da guga
    79. Drycleaner - mai sana'ar wanki da guga
    80. Electricity - wutar lantarki, wutar nefa
    81. Electrician - latirishan, mai gyaran lantarki, ruwaya
    82. Engineering - tsara gine-gine, gyaran kayan lantarki
    83. Engineer - injiya, mai gyaran kayan lantarki, masanin gine-gine
    84. Mechanic - bakanike, makanike
    85. Employer - mai ɗaukar ma'aikata
    86. Employee - wanda aka ɗauka aiki
    87. Farming - noma
    88. Farmer - manomi, manomiya
    89. Gardening - yin lambu
    90. Gardener - mai lambu
    91. Fishing - kamun kifi, su
    92. Fisherman - masunci, mai kama kifi
    93. Fisherwoman - masunciya, mai kama kifi (mace)
    94. Football - kwallon kafa, harkar wasan ƙwallon ƙafa
    95. Footballer - ɗan wasan ƙwallon ƙafa, ɗan ƙwallo
    96. Interpreting - aikin fassara
    97. Interpreter - mai fassara
    98. Translating - aikin fassara
    99. Translator - mai fassara
    100. Labour - aikin ƙwodago, ƙwodago
    101. Labourer - mai aikin ƙwodago, ɗan ƙwodago
    102. Mining - haƙan ma'adanai, tono ma'adanai
    103. Miner - mai haƙan ma'adanai, mai tonon ma'adanai
    104. Painting - fenti, yin fenti
    105. Painter - mai fenti
    106. Plumbing - gyaran hanyar ruwa
    107. Plumber - mai gyaran hanyar ruwa, filamba
    108. Politics - siyasa
    109. Politician - ɗan siyasa, ƴar siyasa
    110. Welding - sana'ar walda
    111. Welder - mai walda
    112. Judge - mai shari'a, alƙali
    113. Lawyer - lauya
    114. Prosecutor - mai bincike a kotu
    115. Librarian - mai zama a ɗakin karatu
    116. Lecturer - lakcara, malamin jami'a, malamar jami'a
    117. Professor - farfesa, shehin malami, malamin jami'a, malamar jami'a
    118. Pupil - ɗalibin firamare, ɗalibar firamare, mai neman ilimi
    119. Student - ɗalibi, ɗaliba, mai neman ilimi
    120. Teacher - malami, malama, mai koyar da karatu
    121. Detective - mai binciken laifi
    122. Guard - mai gadi, mai tsaro
    123. Body guard - mai tsaron mutum, mai take baya
    124. Fire fighter - ma'aikacin kwana-kwana, ma'aikaciyar kwana-kwana
    125. Policeman - ɗan sanda
    126. Policewoman - ƴar sanda
    127. Soldier - soja
    128. Spy - ɗan leƙen asiri, ƴar leƙen asiri
    129. Conductor - kwandesta, yaron mota, karen mota
    130. Driver - matuƙi, direba
    131. Bus driver - matuƙin motar safa, matuƙin bas
    132. Taxi driver - matuƙin tassi
    133. Flight attendant - fasinjojin da za a tafi da su a jirgin sama
    134. Steward - mai lura da fasinjoji a jirgin sama ko na ruwa (namiji)
    135. Stewardess - mai lura da fasinsojoji a jirgin sama ko na ruwa (mace)
    136. Pilot - matuƙin jirgin sama
    137. Cashier - mai kula da harkokin ƙudi, akawu
    138. Director - darakta, mai bada umarni
    139. Manager - shugaba, manaja
    140. Secretary - sakatare
    141. Reception - wajen karɓan baki, karɓan baki
    142. Receptionist - mai karɓan baki
    143. Waiter - mai kawo abinci a otal (namiji)
    144. Waitress - mai kawo abinci a otal (mace)
    145. Athlete - ɗan wasa, ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ɗan wasan motsa jiki, ƴar wasa, ƴar wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ƴar wasan motsa jiki
    146. Coach - mai bada horo
    147. Player - ɗan wasa, ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ɗan wasan motsa jiki, ƴar wasa, ƴar wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ƴar wasan motsa jiki
    148. Trainer - mai bada horo
    149. Trainee - mai karɓan horo
    150. Banker - mai aikin banki
    151. Blacksmith - maƙeri
    152. Builder - mai gini, magini
    153. Bricklayer - magini, mai gini
    154. Butcher - mahauci, barunje, ɗan fawa
    155. Cobbler - mai gyaran takalma
    156. Grocer - mai tsaron shagon abinci
    157. Jeweler - mai siyar da kayan kwalliya
    158. Locksmith - maƙerin kwaɗo
    159. Shepherd - makiyayi, mai kiwo
    160. Shoemaker - baduku, mai haɗa takalma
    161. Tile-setter - mai sa tayils
    162. Watchmaker - maƙerin agogo


Da fatan a na amfanuwa da darusan koyan Turanci da mu ke wallafa a shafin nan. Za mu dakata a nan sai kuma Allah kai mu wani lokaci a gaba mu zo da wani sabon darasi. Ka da dai a manta mu na nan a YouTube da Instagram da Facebook da Twitter domin koyan Turanci cikin harshen Hausa. Mun gode.
إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم