Yadda ake cewa YA KAKE? da Turanci

Assalamu alaikum. Jama'ar wannan shafi. Barkanmu da warhaka. Barkanku da wannan lokaci. Barkanmu da sake kasance daku a wani sabon darasi, wanda acikinsa zamu yi bayanin yadda ake cewa YA KAKE ko YA KIKE ko kuma YA KUKE da Turanci. Shin ko kun san cewa akwai wasu kalmomi da zaku yi amfani dasu a maimakon kalmar beautiful domin bayyana kyan wani abu?


Koyan yadda ake amfani da iri-iren waɗannan kalmomi a lokacin da ake gaisawa, yana da matuƙar amfani, musamman ga ɗalibai da sauran waɗanda suke koyan Turanci.



Ko da babu komai, abu ne mai matuƙar muhimmanci ace kana fahimtar meye mutum yake nufi da wasu kalmomin da yake amfani dasu a lokacin da kuke gaisawa. Hakama sanin kalmomin da yadda ake amfani dasu domin miyar masa da saƙon abu ne mai amfani sosai. Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da launuka da Turanci?


Waɗansu daga cikin kalmomin da ake amfani dasu domin tambayar mutum YA KAKE da Turanci su ne:

    1. what's up?
    2. how is life?
    3. how are you?
    4. how do you do?
    5. how it is going?
    6. how are things?
    7. how are you doing?
    8. how have you been?


Shin ko kun san cewa akwai wasu kalmomin Turanci da zaku iya amfani dasu a maimakon kalmar good domin siffanta kyau ko daɗin abu?


What's up?

A lokacin da ake gaisawa ana amfani da wannan ibara ko ɓangare na jimla, domin tambayar wani ko wata ko wasu YA AKE CIKI ko kuma YA GARI? Misali:


  • Hello, Aliyu. What's up? (Barka dai Aliyu, ya ake ciki?)


How is life?

Wannan kalma ana amfani da ita domin tambayar mutum ya rayuwa. Musamman idan an kwana biyu ba a haɗu ba ko kuma rayuwa ta ɗan yi wahala. A lokacin da kuke gaisawa sai kace wa mutum ya rayuwa? Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da kalmar ENVIOUS?


  • Hello, Ahmad. How is life? (Barka dai Ahmad, ya rayuwa?)


How are you?

Wannan ɓangare na jimla ana amfani dashi domin tambayar wani YA KAKE. Wato YAYA KAKE ko YAYA KIKE ko YAYA KUKE. Wannan ibara ana amfani ita domin tambayar mutum YA YAKE. Kalmar, kalma ce da ake amfani da ita a ƙa'idar Turanci (formal English) wajen gaisuwa.


  • Hello, Aliyu. How are you? (Barka dai Aliyu, ya kake?)


How do you do?

Wannan ɓangare na jimla ana amfani dashi domin tambayar wani YA KAKE. Wato YA KAKE ko YA KIKE ko YA KUKE. Sai dai akan yi amfani dashi domin tambayar wanda yake abokinka ko sa'anka. Amma idan mutumin da ya fika ne ko wani babban mutum sai dai kace masa How are you?


  • Hello, Sadiq. How do you do? (Barka dai Sadiq, ya kake?)


How it is going?

Ana amfani da wannan ɓangare na jimla domin tambayar wata ko wani ko wasu meke faruwa ko ya ake ciki ko ya gari ko kuma al'amura. Shin ko kun san yadda zaku bayyana yanayi da Turanci?


  • Hello, Umar. How it is going? (Barka dai Umar, ya ake ciki?)


How are things?

Ana amfani da wannan ɓangare na jimla domin tambayar wata ko wani ko wasu mutane meke faruwa ko ya ake ciki ko ya gari ko kuma al'amura.


  • Hello, Sameer. How are things? (Barka dai Samir, ya abubuwan?)


How are you doing?

Kamar dai how are you, wannan ɓangare na jimla ana amfani dashi domin tambayar wani ya yake ko wata ya take ko wasu ya suke. Wato yaya kake ko yaya kike ko yaya kuke da Turanci.


  • Hello, Aliyu. What are you doing? (Barka dai Aliyu, ya kake?)


How have you been?

Ana amfani da wannan ɓangare na jimla ne domin tambayar wani ko wasu idan ankwana biyu ba ahaɗuba. Wannan ɓangare na jimla da shi ake amfani domin tambayar mutum a ƙa'idar Turanci (formal English). Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da launuka da Turanci?


  • Hello, Yusuf. How have you been? (Barka dai Yusuf, ya kwana biyu?)


What do you do?

Wannan ɓangare na jimla kuma ba kamar waɗannan suka gabata yake ba, shima dai ana amfani dashi a turanci wajen gaisuwa, amma shi ana amfani dashi domin tambayar mutum mece ce sana'arsa.


  • What do you do Abdoullah? (Wane aiki kake yi Audullahi?)


Wannan shine bayanin yadda ake cewa YA KAKE da Turanci. Idan da mai tambaya, sai ya je ƙasa wajen comment ya rubuta. Haka kuma kar amanta aje channel ɗinmu dake YouTube ayi subscribe tare da taɓa alamar ƙararrawa. Mun gode.
إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم