Assalamu alaikum, jama'a. Barkanmu da warhaka. Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon darasi mai matukar muhimmanci ga dalibai da sauran waɗanda suke sha'awar koyan turanci. Kamar dai kullum, a yau ma muna ɗauke da wani darasi wanda zai gyara wa ɗaliban Turanci wasu kurakurai da suke aikatawa a cikin maganganunsu da rubuce-rubucensu ba tare da sun san cewa sun aikatasu ba.
Yawaita amfani da kalmar VERY, domin a bayyana wata siffa ko gaya ta wata siffa ko wani mataki na wata siffa, kuskure ne. Mu dubi wannan misali mu gani. Idan abu mai kyau ne akan ce masa "good" da turanci. Idan kuma kyan abun sosai ne, sai ahaɗa kalmar "good" tare da "very" domin nuna cewa wannan kyan sosai ne. Misali:
- We went to a very good hotel. (Mun je wani otal mai kyau sosai)
Yawan yin amfani da irin wannan salo na rubutu ko magana, ƙwararru a fagen ilimin harshen Turanci suna ganin cewa kuskure ne. Saboda akwai wasu kalmomi da a karan-kansu suna ƙunshe da wannan ma'ana - waɗanda ba sai anhaɗasu da kalmar VERY ba suke nuna siffa matuƙar. Saboda haka, da ire-irensu yadace ake amfani.
Shin ko kun san cewa akwai wasu kalmomi da zaku iya amfani dasu a maimakon cewa beautiful?
Alal misali, mu ɗauki kalmar "excellent". Ita kaɗai tana ɗaukar ma'anar "very good". Saboda haka, ba sai mun wahalar da kanmu wajen amfani da kalmar VERY da good ba. Kawai maye gurbinsu zamu yi da kalmar excellent. Wacce ita ce kalmar da tafi dacewa da muhallin. Misali:
- We went to an excellent hotel. (Mun je wani otal mai matuƙar kyau)
Kamar haka, kalmar "serene" ita kaɗai take bayar da ma'anar "very calm". Hakama, kalmar "swift" ita kaɗai tana nufin "very fast" kalmar "delighted" ita kaɗai tana nufin "very happy" da dai sauransu.
Shin ko kun san yadda ake tambaya da Turanci?
Saboda haka, idan akwai wata kalma guda ɗaya da take bayar da ma'anar da kalmomin da ake haɗasu da VERY suke bayarwa. To da ita ya dace ayi amfani fiye da wata kalmar tare da VERY. Abun nufi anan shine idan abun yana a matakin da aka saba, siffarsa kaɗai ake ambata. Amma idan matakinsa ya zarce yadda aka saba, sai ayi amfani da kalmar VERY tare da wata siffa domin nuna matakin siffar ya zarce yadda aka saba.
A harshen Hausa, alal misali, maimakon kace "mai kuɗi sosai" zaifi dacewa kace "attajiri". Hakama "ƙaƙƙarfa" a maimakon "mai ƙarfi sosai" ko ace "ƙato" a maimakon "babba sosai". Zamu ga ire-iren waɗannan kalmomi da Turanci tare da kalmomin da ake maye gurbinsu da su.
Shin ko kun san yadda ake amfani da kalmar WOULD?
- Very angry - furious
- Very bad - atrocious
- Very big - huge
- Very cute - adorable
- Very easy - effortless
- Very happy - ecstatic
- Very hard - arduous
- Very risky - perilous
- Very shiny - gleaming
- Very short - brief
- Very shy - timid
- Very strong - powerful
- Very tall - towering
- Very weak - frail
Yanzu kuma ga wasu misalai game da yadda ake amfani da ire-iren waɗannan kalmomi:
Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da launuka da Turanci?
Very angry
Very angry na nufin matuƙar jin haushi ko kuma jin haushi sosai. Akan yi amfani da kalmar furious domin a maye gurbin waɗannan kalmomi biyu. Mu dubi misalai dake tafe:Maimakon kace:
- She is very angry for being late. (Ta ji haushi sosai saboda makarar da tayi)
Sai kace:
- She is furious for being late. (Ta ji haushi sosai saboda makarar da tayi)
Maimakon kace:
- The fans were very angry after the match. (Magoya bayan sun ji haushi sosai bayan tashi daga wasan)
Sai kace:
- The fans were furious after the match. (Magoya bayan sun ji haushi sosai bayan tashi daga wasan)
Shin ko kun san ta yadda zaku fara koyan Turanci?
Very bad
Very bad na nufin wani lamari mara kyau sosai. Wato hali ko yanayi mai muni. Akan yi amfani da kalmar Atrocious domin maye gurbinsu. Mu dubi misalan dake tafe:Maimakon kace:
- At that time the situation was very bad. (A wancan lokacin yanayin yayi muni sosai)
Sai kace:
- At that time the situation was atrocious. (A wancan lokacin yanayin yayi muni ƙwarai)
Maimakon kace:
- At the party the food was very bad. (A wajen bikin abincin ya ɓaci sosai)
Sai kace:
- At the party the food was atrocious. (A wajen bikin abincin ya lalace)
Shin ko kun san yadda ta zaku yi amfani da kalmar ENVIOUS?
Very big
Very big na nufin wani abu babba sosai. Wato ƙatoton abun ko bungurmemen abu. Akan yi amfani da kalmar Huge domin maye gurbin very big. Misali:Maimakon kace:
- Whale is a very big sea creature. (Giwar ruwa halittar ruwa ce mai girma sosai)
Sai kace:
- Whale is a huge sea creature. (Giwar ruwa halittar ruwa ce mai girma sosai)
Whale wani kifi ne mai matuƙar girma wanda yake rayuwa a tekuna. Wannan kifi da Hausa wasu suna kiranshi Uwar ruwa, wasu kuma suna cemasa Giwar ruwa.
Maimakon kace:
- Elephants are very big animals.(Giwaye dabbobi ne masu matuƙar girma)
Sai kace:
- Elephants are huge animals. (Giwaye dabbobi ne masu matuƙar girma)
Very cute
Very cute na nufin kyau sosai. Akan yi amfani da kalmar Adorable domin maye gurbin very cute. Misali:Maimakon kace:
- Her picture was very cute. (Hoton nata ya yi matukar kyau)
Sai kace:
- Her picture was adorable. (Hoton nata ya yi matukar kyau)
Maimakon kace:
- They bought a very cute car. (Sun siyo wata mota mai kyau sosai)
Sai kace:
- They bought an adorable car. (Sun siyo wata mota mai matukar kyau)
Very happy
Very happy na nufin farin ciki sosai. Akan yi amfani da kalmar Ecstatic domin maye gurbin very happy. Misali:Maimakon kace:
- We were very happy to meet you. (Mu na farin ciki sosai da haɗuwa da ku)
Sai kace:
- We were ecstatic to meet you. (Mu na matuƙar farin ciki da haɗuwa da ku)
Maimakon kace:
- You are very happy with the results. (Ka na farin ciki sosai da sakamakon)
Sai kace:
- You are ecstatic with the results. (Ka na farin ciki sosai da sakamakon)
Very hard
Very hard na nufin wahala sosai. Akan yi amfani da kalmar arduous domin maye gurbin very hard. Misali:Maimakon kace:
- Mathematics is a very hard subject. (Lissafi darasi ne mai matuƙar wahala)
Sai kace:
- Mathematics is an arduous subject. (Lissafi darasi ne na cin kwakwa)
Cin kwakwa yana nufin wani aiki mai wahalar gaske. Wato aikin da sai anwahaltu kafin ayisa.
Maimakon kace:
- The homework was very hard. (Aikin gidan yana da wahala sosai)
Sai kace:
- The homework was arduous. (Aikin gidan yana da matuƙar wahala)
Very risky
Very risky na nufin kasada ko haɗari sosai. Akan yi amfani da kalmar Perilous domin maye gurbin very risky. Misali:Maimakon kace:
- Climbing a mountain is very risky. (Hawa tsauni yana da babbar kasada)
Sai kace:
- Climbing a mountain is perilous. (Hawa tsauni yana da babbar kasada)
Maimakon kace:
- Walking in the jungle is very risky. (Tafiya da ƙafa a ƙungurmin daji yana da matuƙar haɗari)
Sai kace:
- Walking in the jungle is perilous. (Tafiya da ƙafa a ƙungurmin daji yana da matuƙar haɗari)
Very shiny
Very shiny yana nufin kyallu ko sheƙi sosai. Akan yi amfani da kalmar Gleaming domin maye gurbin very shiny. Misali:Maimakon kace:
- Our shoes are very shiny. (Takalmanmu suna kyalli sosai)
Sai kace:
- Our shoes are gleaming. (Takalmanmu suna kyalli sosai)
Maimakon kace:
- The new car is very shiny. (Sabuwar motar tana kyalli sosai)
Sai kace:
- The new car is gleaming. (Sabuwar motar tana kyalli sosai)
Very short
Very short yana nufin taƙaitacce sosai. Akan yi amfani da kalmar brief domin maye gurbin very short. Misali:Maimakon kace:
- The explanation is very short. (Bayanin a taƙaice yake sosai)
Sai kace:
- The explanation is brief. (Bayanin a taƙaice yake sosai)
Maimakon kace:
- His statement is very short. (Jawabin nasa taƙaitacce ne sosai)
Sai kace:
- His statement is brief. (Jawabin nasa taƙaitacce ne sosai)
Very shy
Very shy na nufin jin kunya sosai. Akan yi amfani da kalmar timid domin maye gurbin very shy. MisaliMaimakon kace:
- She is very shy. (Tana jin kunya sosai)
Sai kace:
- She is very timid. (Tana jin kunya sosai)
Maimakon kace:
- Why are you very shy? (Me yasa kike jin kunya sosai?)
Sai kace:
- Why are you timid? (Me yasa kike jin kunya sosai?)
Very strong
Very strong na nufin karfi sosai, akan yi amfani da kalmar powerful ko forceful domin maye gurbin very strong. Mu dubi waɗannan misalai dake tafe:Maimakon kace:
- A very strong vehicle knocked down the wall. (Wata mota mai ƙarfi sosai ta zubar da ginin)
Sai kace:
- A powerful vehicle knocked down the wall. (Wata mota ƙaƙƙarfa ta zubar da ginin)
Maimakon kace:
- A very strong animal caught a zebra. (Wata dabba mai ƙarfi sosai ta kama jakin dawa)
Sai kace:
- A powerful animal caught a zebra. (Wata dabba ƙaƙƙarfa ta kama jakin dawa)
Very weak
Very weak na nufin yin rauni sosai. Akan yi amfani da kalmar frail domin maye gurbin very weak. MisaliMaimakon kace:
- The aged man was very weak. (Tsohon ya rauni sosai)
Sai kace:
- The aged man was frail. (Tsohon yayi rauni sosai)
Maimakon kace:
- The patient is very weak after his recovery. (Jikin majinyacin yayi rauni sosai bayan warkewarsa)
Sai kace:
- The patient is frail after his recovery. (Jikin majinyacin yayi rauni sosai bayan warkewarsa)
Waɗannan sune misalan yadda zaka rage yawan amfani da kalmar VERY domin inganta Turancinka. Idan da mai tambaya sai ya je ƙasa wajen comment ya rubuta. Idan Allah yasa mun san amsar tambayarsa, zamu ba shi amsa. Mun gode.