Wasu kalmomi da ake amfani dasu a maimakon GOOD

Mai karatu, Assalamu alaikum. Barka da warhaka. Barka da karatu. Sannunka kuma barka da ƙoƙarin ziyartar shafin nan. Wai shin ko kasan cewa akwai wasu kalmomi da zaka iya amfani dasu a madadin kalmar good? Waɗannan kalmomin zaka iya amfani dasu a kusan duk muhallan da ake amfani da kalmar good ba tare da aukuwar canzawar ma'anar ba.


Shin ko kun san cewa akwai wasu kalmomi da zaku iya amfani dasu a maimakon cewa beautiful?


Ƙwarai tabbas! Akwai wasu kalmomi da zaka iya amfani dasu a muhallan wasu kalmomin ba tare da aukuwar canzawar ma'ana ba. Kafin muyi nisa a darasin, mu dubi waɗannan misalai dake tafe, domin samun ginshiƙin fahimtar yadda abun yake.


    1. Aliyu has a good handwriting. (Aliyu yana da rubutu mai kyau)
    2. Aliyu has a nice handwriting. (Aliyu yana da rubutu mai kyau)
    3. Fatima bought a good dress. (Fatima ta siyo kaya mai kyau)
    4. Fatima bought a nice dress. (Fatima ta siyo kaya mai kyau)


Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da launuka da Turanci?


Jimloli biyun farko dake sama, ma'anarsu ita ce 'Aliyu ya iya rubutu sosai'. Sannan kuma idan muka lura da misalan, zamu ga cewa a jimlolin mun sauya kalmar good da nice, waɗanda kalmomi ne da a wasu lokutan suke ɗaukar ma'ana iri ɗaya. Mun yi amfani da kalmomi biyu mabambanta domin bayyana kyawun rubutun Aliyu da kyan kayan Fatima, amma hakan bai canza wa jimlolin ma'ana ba.


Akwai kalmomi mabambanta furuci ko harafi dake ɗaukar ma'ana daya. Irin waɗannan kalmomi su ake kira da synonyms


A jimlolin farko, mun yi amafani da kalmomin good. A jimloli na biyu kuma mun yi amfani da kalmomin nice. Duk da cewa kalmomi biyu ne mabambanta sauti da zubin harufa, kalmomi ne da suke ɗaukar ma'ana iri ɗaya a mafi yawan lokaci.


Shin ko kun san ta yadda zaku fara koyan Turanci?


Yanzu kuma zamu shiga darasin gadan-gadan. Sai dai zamu fara bayanin ne da kawo ma'anar kalmar good.


Ma'anar kalmar 'GOOD'

Kalmar good, kalma ce ta siffa, wacce ake amfani ita domin siffanta hali ko yanayin wani mutum ko wani abu. Ƙari akan haka, kalmar tana da ma'anoni dadama. Wasu daga cikin ma'anoninta sune: kalmar tana nufin abu mai kyau; tana nufin haɗaɗɗen abu; tana nufin abu mai daɗi; tana nufi abu mai amfani; tana nufin abu mai lafiya, kamar yadda zamu gani a misalai dake tafe.


Misali:

    1. She wore a good dress at the party. (Ta yi shiga mai kyau a wajen bikin)
    2. He came up with a good idea. (Ya zo da wani tunani mai kyau)
    3. The restaurant was good. (Shagon siyar da abincin ya haɗu)
    4. The guy was good. (Matashin haɗaɗɗe ne)
    5. The tour was good. (Yawon buɗe idon yayi daɗi)


Idan muka dubi waɗannan misalai dake sama, zamu ga yadda kalmar good tazo. Sannan a kowace jimla daga cikin misalan kalmar tazo da wata ma'anar ta daban - ko dayake gaba ɗaya, idan muka lura zamu ga cewa ma'anonin sun kusa zuwa ɗaya.


Bayan waɗannan misalai na sama, ga wasu kalmomi dake tafe a ƙasa waɗanda suke ɗaukar ma'ana iri ɗaya da kalmar good. Haka kuma kana iya amfani dasu domin maye gurbin kalmar good a gurare da dama. Kamar yadda zamu gani a misalan dake tafe a ƙasa.


Shin ko kun san me kalmar Envious take nufi da kuma yadda zaku yi amfani ita?


Kalmomin sune:

    1. Amazing
    2. Excellent
    3. Good
    4. Handsome
    5. Nice


Misali:

    1. She wore a nice dress at the party. (Ta yi shiga mai kyau a wajen bikin)
    2. He came up with an amazing idea. (Ya zo da wani tunani mai matuƙar kyau)
    3. The restaurant was excellent. (Shagon siyar da abincin ya haɗu sosai)
    4. The guy was handsome. (Matashin haɗaɗɗe sosai ne)
    5. The tour was amazing. (Yawan buɗe idon yayi matuƙar ƙayarwa)


Waɗannan kalmomin wasu ne daga cikin ire-iren kalmomin da ake amfani dasu domin maye gurbin kalmar good. Akwai waɗansu kalmomin da akan yi amfani da su domin maye gurbin good ba tare da canzawar ma'anar jimla ba. Sai dai su waɗannan suna nuni ne ga kyau matuƙa gaya, wato matuƙar kyau ko kuma kyau sosai


Abin lura anan shine, su waɗannan kalmomin suna nuna kyau ne matuƙa. Wato idan kace good, yana nufin mai kyau ko mai daɗi ko mai ƙayatarwa. Amma idan ka ɗakko ɗaya daga cikin waɗancan kalmomin na sama zasu baka ma'anar kyawun gaske ko daɗin gaske ko kyau sosai ko daɗi sosai ko matuƙar kyau ko kuma matuƙar daɗi. Kana iya cewa very good ko so good. Amma ba zayyiwu kayi amfani da kalmar very ko so tare da ɗaya daga cikin waɗancan kalmomin dake sama ba.


Misali, kana iya cewa:


  • She wore a very good dress at the party. (Ta yi shiga mai kyau sosai a wajen bikin)

Hakama, kana iya cewa:


  • She wore a very nice dress at the party. (Ta yi shiga mai kyau sosai a wajen bikin)

Amma, ba zayyiwu kace:


  • She wore a very amazing dress at the party. (Ta yi shiga mai matuƙar kyau a wajen bikin)

Hakama, ba zayyiwu kace:


  • She wore a very excellent dress at the party. (Ta yi shiga mai matuƙar kyau a wajen bikin


Shin ko kun san ta yadda zaku fara koyan Turanci?

Gwaranci ne, amfani da ire-iren waɗannan kalmomi tare da so ko very a harshen Turanci. Domin waɗannan kalmomin ba a nuna matukar gayarsu da kalmar very ko kalmar so. A maimakon haka, suna da wasu kalmomi da ake amfani dasu domin nuna gayar matukarsu. Kalmomin da ake amfani dasu domin nuna gayar waɗannan kalmomin wasu daga cikinsu sune: absolutely, certainly, extremely, really, quite da sauransu.


Bari mu ɗauki ɗaya daga cikin waɗannan kalmomin, mu yi amfani dasu a waɗannan misalai dake tafe. Misali:


    1. She wore an extremely amazing dress at the party. (Ta yi shiga mai matuƙar kyau a wajen bikin)
    2. She wore an extremely excellent dress at the party. (Ta yi shiga mai kyau matuƙa a wajen bikin)


Duk inda kalmar extremely tazo a waɗannan misalai na sama - zaka iya canzata da ɗaya daga cikin ire-irenta, wato su: absolutely, certainly, really da sauransu. Misali, bari mu canza kalmar extremely da really:


    1. She wore a really amazing dress at the party. (Ta yi shiga mai matuƙar kyau a wajen bikin)
    2. She wore a really excellent dress at the party. (Ta yi shiga mai kyau matuƙa a wajen bikin)


Shin ko kun san yadda zaku yi amfani da launuka da Turanci?

Babu mamaki a samu wasu kalmomin dake da ma'ana irinta da beautiful waɗanda watakila basa daga cikin kalmomi biyar da muka lissafo a sama. To yana da kyau, idan anci karo dasu, a fahimci yadda ake amfani dasu a jimla. Gwarancine rashin yin amfani da kalma a bisa muhallin da ya dace da ita acikin kowace irin al'umma ce. Domin kowace al'umma akwai muhallin da take aza kalmominta a cikin jimla.


Muna masu rufe wannan darasi da waiwaye adon tafiya, wanda shine bambance wace kalmace ake amfani da ita tare da very da kuma waɗanda ba a amfani dasu tare da very. Sannan kuma, su waɗancan kalmomin guda biyar suna nuna matuƙar kyau fiye da yadda kalmar beautiful take nunawa. Bayanai game da yadda ake amfani da waɗannan kalmomi sun gabata a sama tare misalai.


Zamu dakata anan muna fatan Allah yasa a amfana da abubuwan da ake karantawa. Mun gode sai wani lokaci.

إرسال تعليق (0)
أحدث أقدم